Afghanistan: Dusar kankara ta hallaka mutane 25
February 19, 2024![Zubar dusar kankara a Afghanistan](https://static.dw.com/image/64440270_800.webp)
Talla
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da zubar dusar kankara sun janyo zaizayar kasa a gundumar Nuristan a gabashin Afghanistan wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 25 yayin da wasu da dama kuma suka makale a cikin baraguzai
Ana ci gaba da aikin ceto inda ake kyautata tsammanin yawan wadanda suka rasu na iya karuwa.
Aghanistan ta saba da tsananin sanyi sai dai a bana an sami jinkiri fara zubar dusar kankarar.