1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan: Taliban na kara samun nasara

Zainab Mohammed Abubakar RGB
August 12, 2021

Wasu kasashen Turai sun yanke shawarar dakatar da mayar da 'yan kasar Afghanistan da suka nemi mafaka gida a sakamakon munin fadan da ake da mayakan Taliban.

Afghanistan | Bildergalerie | Truppenabzug
Hoto: NOORULLAH SHIRZADA/AFP/Getty Images

Bayan Jamus da Netherlands da a farkon wannan makon suka sanar da dakatar da korar 'yan Afghanistan da ba su da takardun shaidar zaman kasa, ita ma Faransa ta bi sahu. Wannan na da alaka da halin da kasar ta tsakiyar Asiya ta tsinci kanta a ciki a cewar sanarwar ma'aikatar Faransa.

Tun daga farkon watan Yuli ne, aka daina iza keyar 'yan Afghanistan zuwa kasarsu ta asali, kasar da a yanzu haka ake cigaba da fafatawa tsakanin mayakan Taliban  da dakarun gwamnatin kasar. Wannan rikici ya samo asali ne tun lokacin da aka zartar da janye dakarun kasa da kasa daga wannan kasa da yaki ya daidaita a tsakiyar watan Afrilu.

Gwamnatin Afghanistan ta yi wa Taliban tayin sulhuHoto: Rahmat Gul/AP/picture alliance

Mayakan Taliban sun cimma nasarar kwace madafan ikon manyan biranen gundumomi 10 daga cikinb 34 na Afghanistan. A ranar Larabar da ta gabata, Jamus da Netherland suka sanar da tsayar da koran 'yan Afghanistan, da aka hanasu mafakar siyasa. Jakadun Kungiyar Tarayyar Turai da ke Kabul da was kungiyoyi 26 ne suka nemi yin hakan.

Karin Bayani: Taliban ta karbe ikon Ghazni kusa da Kabul

A wannan Alhamis ce, Taliban ta kwace babban birnin gunduma ta 10 na Ghazni mai tazarar Kilomita 130 daga yankin Kudu maso Yammacin birnin Kabul, fadar gwamnatin kasar. Majiya daga birnin ta shaida wa manema labaru cewar, ana cigaba da gumurzu a garuruwan da ke wajen birnin.

Dubbai da suka tsere wa rikici na cikin mawuyacin haliHoto: Omid Deedar/DW

Gwamnatin Afghanistan da ma jami'an tsaronta sun ki yin martani dangane da halin da ake ciki na wannan dauki ba dadi da ya kara ta'azzara a 'yan kwanakin nan. Sai dai Shugaba Ashraf Ghani na kokarin yin martani da dakaru na musamman da mayakan sa-kai da karfin jiragen yakin Amirka gabanin ficewar Amirkan da NATO a karshen wannan watan.

Karin Bayani: Sharhi: Taliban na cin karenta babu babbaka

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya sanar da cewar, akwai yiwuwar haduwarsa da shugaban 'yan Taliban, a wani mataki na ceto Afghanistan daga halin da take ciki. A yanzu haka Turkiyya na da sojoji a Afghanistan a bangaren rundunar tsaro ta NATO  kuma ta yi alkawarin taimakawa a kula da filin saukan jirgin Kabul, ko bayan ficewar rundunar kasa da kasar a karshen wannan wata na Augusta.

A daidai lokacin da ake cigaba da luguden wuta kuma harkokin tsaro ke kara tabarbarewa a Afghanistan, gwamnatin Kabul ta yi tayin raba madafan iko a tattaunawar sulhu da Taliban da ke gudana a birnin Doha na kasar Qatar, a wani mataki na kawo karshen fadan da ake, a cewar majiyar gwamnati a wajen tattaunawar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani