1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfghanistan

Shekaru biyu na kunci a mulkin Taliban

August 15, 2023

Shekaru biyu kenan cif da 'yan Taliban suka karbi mulkin kasar Afghanistan. Sai dai duk da irin fatan da aka yi na samun gwamnati mai sassaucin ra'ayi ba kamar irin ta shekarun 1990 ba

Hoto: Ebrahim Noroozi/AP Photo/picture alliance

Sakamakon tsattsauran ra'ayi na mahukuntan wannan lokaci ana muzgunawa 'yan kasar tare da tauye hakkin dan Adam, baya ga jefa masu fafutikar kare hakkin jama'a da jefa su cikin hadari. Wannan lamari ya tilasta wa kashi 80 cikin dari na 'yan jarida a kasar yin watsi da aikinsu. 

Zalunci, kame-kamen mutane ba bisa ka'ida ba, cin zarafin mata, da kisa ba bisa ka'ida ba, kadan ne daga cikin ababen da ke tayar da hakalin kasashen duniya tun bayan da 'yan Taliban suka karbi mulki a Afghanistan inda suka mayar da kasar karkashin tsauraran dokokin Islama.

Hoto: Ali Kaifee/DW

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa ciki har da Human Rights Watch, sun ce akwai gagarumar damuwa a game da makomar 'yanci da walwalar jama'a a Afghanisthan musamman 'ya'ya mata da ke cikin gagarumar barazana tsawon shekaru kenan. 

Rukunin farko dai na wadanda suka fara gamuwa da ukubar 'yan Taliban sune mata da 'yan mata wadanda gwamnatin ta yi masu tsattsauran ra'ayi ta bijiro da sabbin dokoki da suka tilasta masu sanya Nikabi tare kuma da haramta masu zurfafa ilimi, wanda ke zama gishirin rayuwa. Duk da irin gwagwarmayar da kungiyoyin mata na ciki da wajen kasar suka sha, da kuma matsin lamba daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, 'yan Taliban sun ci gaba da kasancewa kan bakansu a game da batun ba wa mata wannan 'yanci na neman ilimi kamar 'yan uwansu maza.

Hoto: ALI KHARA/REUTERS

Roya Amiry wata malamar makaranta a birnin Herat ta bayyana damuwa a kan yadda matakin zai haifar da cikas ga rayuwar mata.

"Idan 'yan mata ba su samu zarafin zuwa neman ilimi ba, ba za su iya su zama kwararrun likitotci ba, ko injiniyoyi, ko 'yan jarida ko kuma malaman makaranta ba. Idan mace ba ta samu ilimi ba to makomar rayuwarta ta lalace''.

Ko baya ga fannin ilimin 'ya'ya mata, gwamnatin ta Taliban ta dauki wasu tsauraran dakoki na soke gudanar da wasu ayyuka a kasar, lamarin da ya jefa mata sama da 60,000 rasa madogara. Daga shekarar 2021 zuwa wannan lokaci dokar ta bigi masu shagunan gyaran gashi da kwalliyar mata, kuma wannan mata na daya daga cikin wandada lamarin ya saka cikin garari.

Hoto: Ali Khara/REUTERS

"Zuwan wannan gwamnati mun rasa ayyukanmu, abin da ya rage mana kawai mu gudu daga wannan kasa domin bamu da wata hanya ta samun kudade. Ba na iya ciyar da 'ya'yana kuma ba ni da wani da za taimakamin domin mijina ya rasu''.

Wadannan take-take na gwamnatin Taliban ya sa kasashe da kungiyoyin kasa da kasa kakaba wa Afghanistan takunkumai, lamarin da a cewar kungiyar Save the Children ya haddasa matsananciyar yunwa a kasar. Wani bincike na kungiyar ya nunar da cewa kashi uku cikin hudu na yaran Afghanista ba sa samun isashen abinci baya ga dama kashi 58 cikin dari na iyalai na cikin mawuyacin hali sakamakon matsanancin fari da kasar ta fada ciki yau shekaru 30.

Hoto: WAKIL KOHSAR/AFP/Getty Images

A cewar Majalisar Dinkin Duniya katse ba wa kasar ta Afghanistan tallafi bayan zuwan gwamnatin Taliban ya jefa mutane miliyan hudu ciki har da yara masu kasa da shekaru biyar miliyan uku cikin matsalar karancin abinci, lamarin da ke haddasa tamowa da wasu cutuka masu kisa.

Wannan matsanancin hali da gwamnatin Taliban ta jefa al'ummar Afghanistan ya kai gwamnatin Jamus bijiro da wani shirin na ba wa 'yan kasar da ke cikin halin matsi mafaka. Sai dai tsarin na Berlin wanda ya jibanci kabar mutane 14,000 a cikin shekarun biyar galibinsu mata da ke cikin halin tsaka mai wuya ya gamu da turjiyar gwamnatin Taliban wacce ke dari-dari wajen ba wa wadanda za su ci gajiyar tsarin izinin fita daga kasar.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Jamus daga cikin 'yan Afghanistan 30,000 da ta ba wa izinin zuwa kasar domin samun saukin rayuwa, mutum 56 ne kadai suka samu amincewar 'yan Taliban, yayin da sauran ke cikin jira wasunsu kuwa aka yi watsi da takardunsu.