Afghanistan ta ce ta kwato birnin Kunduz
October 1, 2015Hukumomin Afghanistan sun bayyana cewar sun yi nasarar sake mayar da garin Kunduz da ke Arewacin kasar karkashin kulawarsu, bayan da suka shafe daren Laraba zuwa wannan Alhamis suna bata kashi da 'yan Taliban. Mataimakin ministan cikin gida Afghanistan Ayoub Salangi ya bayyana cewar sun samu tallafi sojojin Amirka, kafin su cimma burinsu na fatattakar masu tsattsauran ra'ayin Islama.
Tun dai a ranar Litinin da ta gabata ne dai 'yan taliban suka kutsa Kunduz tare da mamaye wannan birni, lamarin da ya haddasa tsaiko a dabarun gwamnati na gannin bayan tsagerun.
Sai dai kuma wani kakakin 'Yan taliban Zabihullah Mujahid ya karyata cewar an karbe ikon Kunduz daga hannunsu, inda ya ce suna ci gaba da kalubalatar sojojin gwamnatin Afghanistan. Sannan akasarin sassan wannan birnin na hannunsu.