1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan: Taliban ta kashe 'yan sanda

October 30, 2017

Jami'ai a Afghanistan, sun ce wasu mayakan Taliban sun kaddamar da wani hari da ya halaka 'yan sanda tara a gabashin lardin Ghazni.

Afghanistan Selbstmordanschlag in Gardez
Hoto: Getty Images/AFP/F. Zahir

Jami'ai a kasar Afghanistan, sun ce wasu mayakan Taliban sun kaddamar da wani hari da ya halaka 'yan sanda tara a gabashin lardin Ghazni. A cewar mai magana da yawun gwamnan lardin, Arif Noori, akwai wasu 'yan sanda hudu da suka jikkata aharin na wannan Litinin.

Jami'in ya kuma ce jami'an tsaron, sun yi nasarar kashe 'yan Taliban din su bakwai tare da raunata wasu, a musayar harbe-harbe na sa'a guda da ta wakana tsakanin bangarorin biyu. Ko da yammacin wannan Lahadi ma dai mayakan na Taliban, sun afkawa wani shingen jami'an tsaro dake lardin Zabul inda aka rasa 'yan sanda akalla shida.