1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka a jaridun Jamus 01.12.2023

Usman Shehu Usman M. Ahiwa
December 1, 2023

Janye dokar hukunta safarar bakin haure a Nijar da kawo karshen ayyukan MDD a Mali da takaddamar kasashen Yamma da wasu shugabannin Afirka sun dauki hankalin jaridun Jamus.

Bakin haure a kan hanyar neman shiga Turai daga Agadez
Bakin haure a kan hanyar neman shiga Turai daga AgadezHoto: Jerome Delay/AP/picture alliance

A wannan makon jaridar die Welt ce za ta bude mana sharhunan jaridun na Jamus, inda ta ce Jamhuriyar Nijar ta jingine yarjejeniya tsakaninta da kungiyar EU kan batun 'yan gudun hijira. Sai jaridar ta dora cewa, Nijar ta kasance babbar abokiyar huldar Turai wajen dakile kwararar bakin haure daga Afirka. Musamman a lokacin tsohuwar shugabar gwamnati Jamus Angela Merkel ke mulki, ta maida Nijar abun yabo bisa kyakkyawar hulda da aiki tare da ake yi da Nijar kan ‘yan gudun hijira. Amma a yanzu gwamnatin mulkin soja ta yi watsi da dokar da ke da matukar muhimmanci musamman ga shugabannin Turai.  A zamanin Angela Merkel ta yaba wa NIjar kasar da ke dauke da kimanin bakin haure dubu 100 da ke kan hanyar shiga kasar Libiya. A lokacin ne Jamhuriyar Nijar ta kafa doka mai hana safarar mutane musamman masu rakiya da tallafa wa baki masu son zuwa Turai. 

Tafiyar kasada cikin hamadar SaharaHoto: DW

Za mu dora da jaridar die Tageszeitung, wacce itama ta yi batun kan Nijar da makwabtanta. Jaridar ta ce kawo karshen ayyukan Majalisar Dinkin Duniya daga Mali da takunkumin da aka kakaba wa Nijar na kara wa ayyukan kungiyoyin agaji na kasa-da-kasa wahala. Jaridar ta ce a iya cewa ayyukan MDD kansu a yanzu suna neman zama tarihi a yankin, musamman rundunar MINUSMA a kasar Mali. Domin kuwa zuwa karshen watannan yakamata dukkanin dakarun MDD su fice daga kasar Mali, kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a watan Yuni. Bayan da gwamnatin sojan Mali ta ce su tattara su fice daga kasar ta.  Kai tuni ma dai sansanonin MDD 12 da ke cikin kasar Mali, duk tuni aka rufe su. Wannan ficewar dakarun kasashen Yamma daga Mali ya kawo babbar barazana ga kungiyoyin farar hula da ke aikin agaji a yankin na Sahel.

Hoto: Florian Gaertner/photothek/picture alliance

Jaridar Süddeutsche Zeitung ita kuwa ta kalli wannan takaddamar kasashen Yamma da wasu shugabannin Afirka ne ta wata fuska daban. Jaridar na mai cewa tun da jimawa masu mulkin kama karya sun fi son manufofin Faransana Afirka na kunshi cin hanci da rashawa. Yanzu irin wannan tsarin ya shiga cikin yanayi na mai yuwa musamman Turawan mulkin mallaka na Faransa tare da iyalan Bongo wato tsohon shugaban kasar Gabon, wanda masu bincike ke kara bayyana yawan dukiyarsa a Paris. Jaridar ta ce yayin da mutane irin su iyalan Bongo suka yi ta samun yabo da yin mulkin da suka ga dama a kasar, yanzu komai na fitowa a fili cewa wani tsari ne na kawar da ido da turawan kasar da ta yi Gabon mulkin mallaka suka yi don kashe muraba da ake yi, wanda kuma ga irin wadannan shugabannin kama karya suka fi so Faransa na rufa musu baya suna ta kwasar dukiyar ‘yan kasashensu.