1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan Afirka

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
July 3, 2020

Mutuwar fitaccen mawakin fafutukar kasar Habasha da batun maganin coronavirus da cin zarafin mata a Afirka ta Kudu, sun dauki hankulan jaridun Jamus a wannan makon.

Äthiopien Hachalu Hundessa, ermordeter Künstler
Mawaki Hachalu Hundessa da aka halaka a HabashaHoto: Leisa Amanuel

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta wallafa labarinta mai taken "Akwai tashe-tashen hankula da zubar da jini a Habasha, hakan na nufin Firaminista Abiy Ahmed ya gaza sasanta kabilu kenan?" Mawakin fafutukar Hachalu Hundessa dai ya samu kyakkyawar jana'iza wadda gwamnati ta dauki nauyin gudanarwa a filin wasan kwallon kafa da ke mahaifarsa mai suna Ambo. Gidan talabijin na kasar ya haska bikin jana'izar kai tsaye, kana jami'an sojoji da na 'yan sanda sun yi masa fareti yayin jana'izar da aka gudanar a ranar Alhamis.

Da maraicen ranar Litinin ne dai aka bindige mawakin na Habashan Hachalu Hundessa a birnin Addis Ababa, daga bisani ya ce ga garinku nan a babban asibitin Tirunesh Beijing da ke fadar gwamnatin. Babu wanda ya san wacce kabila ce ta aikata kisan gillar da aka yi wa mawakin wanda dan kabilar Oromo ne. Kabila Oromon ce dai mafi girma a kasar, wadanda kuma ke kokawa da cewa ana yi musu danniya a harkokin kasar. Kawo yanzu dai an cafke wasu da ake zargi da hannu a kisan mawakin.

Duk da haka zanga-zanga ta barke a biranen Habashan da ke yankin gabashin Afrika, kuma kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane sama da 90. A ranar Talata ne dai, gwamnatin framinista Abiy Ahmed ta yanken hanyoyin sadarwa na internet  a fadin kasar.

Tazargade a matsayin maganin coronavirusHoto: DW/B. Darame

Ita kuwa jaridar "Die Welt" sharhi ta yi a kan ganyen nan na Tazargade mai taken "Waraka mai cike da al'ajabi a Afirka." An yi ittifakin cewar ganyen Tazargade na warkar da cutar coronavirus a Afirka, dalili kenan da ya sa ake samun karin kasashen da ke neman ganyen. Ana sarar ganyen daga wajen kananan manoma. Ganyen dai yana da daci sosai a cewar wadanda suka sha.

John Abesalie mai shekaru 54 da ya saba shan ganyen na Tazargade idan yana zazzabi, ya dukufa wajen shansa a kowace rana tun bayan da ya ji cewar yana hana mutum kamuwa da coronavirus, kuma ta kan warkar da wanda ke da cutar. Wannan manomi da ke faftukar neman abin da zai ciyar da iyalinsa a kowace rana, yana cike da farin cikin cewar, a kalla sun tsira daga annobar coronavirus. A garin Thornhil da ke gabar teku a Afrika ta Kudu, Tazargaden kusan shi ne ciyawarsu, ganyen da a yanzu ya yi kaurin suna a kasashen duniya ciki har da Jamus, inda ake ci gaba da gudanar da binciken sahihancinsa wajen yakar kwayar cutar corona.

Yaki da cin zarafin mata a Afirka ta KuduHoto: AFP/R. Bosch

A Afirka ta Kudu kuwa matsalar cin zarafin mata ne ya sake kunno kai daga bangaren maza da shan barasa ta zame musu tamkar shan ruwa. Jaridar Die Tageszeitung ta ce tun bayan da aka dage dokar hana sayar da barasa da aka sanya a baya saboda cutar coronavirus, matsalar cin zarafin mata yara ya karu. A kalla an yi wa mata da yara kanana 21 kisan gilla, tun bayan dage dokar.

Wannan dai ita ce annoba ta biyu bayan coronavirus, da kasar ta Afirka ta Kudun ke fama da ita, wato kwankwadar barasa kafin afkawa matan. Wannan hali da ake ciki dai ya janyo hankalin duniya, abin da ya sanya hana sayarwa da kasar barasa har na tsawon watanni biyu, daga ketare.

An dauki matakin ne domin kare cunkoson jama'a wajen shan barasar, inda ta nan ne coronavirus za ta yadu a sauwake, da kuma taimakawa asibitoci kaucewa jinyar wadanda ke fama da rashin lafiyar da ke da alaka da shan barasa ko kuma maye.