1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Afirka a Jaridun Jamus 28.06.2024

Ahmed Salisu M. Ahiwa
June 28, 2024

Zanga-zangar matasa a kan tsarin haraji a Kenya da wadda daliban makarantun kasae Senegal suka yi a mako, sun dauki hankalin jaridun kasar Jamus masu nazari kan kasashen nahiyar Afirka.

Matasa masu zanga-zanga a birnin Nairobin Kenya
Matasa masu zanga-zanga a birnin Nairobin KenyaHoto: Monicah Mwangi/REUTERS

Bari mu fara sharhunan jaridun Jamus din nahiyarmu ta Afirka da sharhin da jaridar Welt Online ta rubuta, inda ta yi tsokaci a kan znaga-zangar da matasa a Kenya suka shafe kwanaki suna yi kan kudurin dokar haraji da majalisar dokokin kasar ta amince da shi. Jaridar ta ce a ranar Talatar da ta gabata dubban matasa suka fantsa kan titi dun nuna rashin amincewarsu da dokar wadda shugaban ya janye tare da mayar da ita majalisa don sake dubawa, sai da wasu daga cikin matasan da ke zanga-zangar akalla 23 sun rasa ransu. To sai dai duk da haka inji jaridar, matasan sun ci gaba da yin zanga-zangar ta lumana inda suka yi wa majalisar dokokin kasar tsinke don aikewa da sakonsu na kin amincewa da kudurin dokar wanda suka son a yi watsi da shi baki daya.

Sharhin da jaridar Zeit ta rubuta ma dai kan zanga-zangar adawa da dokar haraji a Kenya din ne, inda ta ce bayan shan matsin lamba, shugaban kasar William Ruto ya mika wuya inda ya janye dokar tare da mayar da ita majaliusa don sake dubata. Jaridar ta rawaito shugaban yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai yana cewar al'umma sun magantu don hakan mun jaye don yi mata gyara tare kuma da yin zama na musamman da matasan kasar don tattaunawa kan kunshin dokar don samar da maslaha. A lokacin da ya mika wuya inji jaridar, kimanin mutane 300 sun jikkata yayin da wasu da suka haura 20 suka rigamu gidan gaskiya.

Ita ma da jaridar Die Tageszeitung sharhin nata ya karkata ne kan kasar ta Kenya, sai dai ta mayar da hankali ne kan 'yansanda da Kenya din ta aike da su zuwa kasar Haiti don su taimaka wajen tabbatar da doka da oda a kasar. Jaridar ta ce shugaban Kenya din ya yi jawabi na bankwana da 'yansanda su kimanin 400 daidai lokacin da ake tsaka da zanga-zanga a kasar kan dokar haraji da batutuwa da suka danganci cin hanci da rashawa. Sharhin ya kara da cewar gabannin tafiyar 'yansanda dai, an yi ta dage fara aikin saboda batu na kudin da za a yi amfani da su wajen aikin bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shirin. Kudin dai sun kai dalar Amirka 200 wanda 'yan majalisar dokokin Amurka na Republican suka ki amincewa da sakinsu batun da ya sanya kila a takaita aikin 'yan sanda zuwa watanni shidda kacal.

Zanga-zangar da daliban jami'a a kasar Senegal ke yi ya nuna irin halin da daliban jami'a ke ciki a Afrika. Wannan shi taken sharhin jaridar Frankfurter Allgemeinezeitun na wannan makon. Jaridar ta ce shekarar 1997 ce daliban jami'an nan ta ENS suka yi yajin cin abinci saboda yanayin da harkar karatu ya shiga da kuma makomarsu bayan kammala karatun. Jarida ta ce a baya inda mutum ya gama jami'ar to yana da tabbacin samun aiki sai dai abubuwa sun sauya yanzu wanda haka shi ne hakikanin abin da ke faruwa da daliban da suka kammala jami'a a kasashen Afrika da dama. Jaridar ta ce wannan batu na da nasaba da irin tsarin da Bankin Ba da Lamuni na Duniya IMF da Bankin Duniya suka yi a kasar bayan da ci bashi wanda ya kai ga haifar da matsaloli a bangarori daban-daban ciki har da batun samun aiki.