1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Jaridun Jamus: Sharhi kan corona a Afirka

Suleiman Babayo LMJ
December 17, 2021

Batun annobar corona nau'in omicron da riga-kafin cutar da kuma karuwar zazzabin cizon sauro a Afirka, sun mamaye sharhunan jaridun Jamus kan Afirka na wannan makon.

Südafrika Omicron Impfkampagne
Afirka na baya wajen yin allura riga-kafin corona a duniyaHoto: Jerome Delay/AP Photo/picture alliance

A sharhinta, jaridar die Tageszeitung ta ce sabon nau'in cutar coronavirus da ake kira omicron ya karfafa matakin yin riga-kafi, kuma samun riga-kafin zuwa mataki na uku na karfafawa na zaman hanyar dakile sabon nau'in cutar. Mahukunta a Afirka ta Kudu sun tashi tsaye kan yin riga-kafin, inda masana ke ci gaba da nuna muhimmancin yin ta. Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce nahiyar Afirka tana sahun baya a riga-kafin annobar ta coronavirus, yayin da manyan kasashen Turai da wadanda suke sahun gaba a karfin tattalin arziki suka yi nasarar yiwa sama da kaso 40 cikin 100 na al'ummarsu riga-kafin. Jaridar ta ce kasso bakwai cikin 100 kacal na al'umma nahiyar Afirka ne, suka yi riga-kafin. Majalisar Dinkin Duniya tana muradin ganin kaso 70 cikin 100 na al'ummar duniya sun yi riga-kafin zuwa watan Satumbar shekara mai zuwa ta 2022. Kungiyar Tarayyar Turai tana taimakawa kasashe masu tasowa da suka hada da na Afirka wajen samun rigakafin da ake bukat.

Amfani da gidan sauro mai magani, kan taimaka wajen rage zazzabin cizon sauroHoto: Yanick Folly/AFP

A daya bangaren jaridar Der Tagesspiegel ta yi sharhi mai taken ana kara samun yaduwar cutar zazzabin cizon sauro malaria, yayin da ake fama da yaki da annobar cutar coronavirus. Jaridar ta ce an samu koma baya kan yaki da cutar zazzabin cizon sauro da ake samu a kasashe masu zafi galibi na Afirka da karuwar mace-mace, sakamakon cutar kamar yadda alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya WHO suka nuna kuma hakan na da nasaba da annobar cutar coronavirus da ke ci gaba da daukar hankali. A shekarar da ta gabata ta 2020 an samu alkaluma na kamuwa da zazzabin cizon saura milyan 241, inda aka samu kari na alkaluma milyan 14 idan aka kwatanta da shekara ta 2019. Sannan yawan mutuwa daga cutar ta zazzabin cizon sauro ya karu da kimanin 70,000, inda aka samu mutuwar mutane dubu 627. Hukumar ta WHO ta ce galibin mace-macen za a iya kauce musu, amma aka gaza saboda annobar cutar coronavirus da ake fuskanta.
A nata bangaren jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhin da ke cewa kasar Gambiya ta wuce gwajin farko kan tsara zabe cikin kwanciyar hankali, yayin da ake ganin juyin mulki a wasu kasashen yankin yammacin Afirka. Sakamakon zaben ya nuna Shugaba Adama Barrow ya samu nasara da kaso 53 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Kuma wannan ke zama zabe na farko tun bayan kawo karshen mulki kama-karya na tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh wanda ya yi mulki daga shekarar 1994 zuwa shekara ta 2017, inda ya fara a matsayin soja bayan da ya jagoranci juyin mulki sannan daga bisani ya rikide zuwa dan siyasa.

Shugaba Adama Barrow ya samu nasarar yin tazarce a matsayin shugaban GambiyaHoto: Leo Correa/AP Photo/picture alliance