Sharhunan Jaridun Jamus akan Afirka
February 12, 2021Za mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung da ta rubuta sharhinta mai taken WTO ta samu shugaba mai kazar-kazar da za ta kawo sauyi. Jaridar ta ce Washington ta marawa Okonjo-Iweala baya, 'yar Najeriyar na zaman mace ta farko daga Afirka da za ta zama shugabar kungiyar Ciniki ta Duniya. Zai kasance tamkar riba biyu. Bayan da Amirka karkashin sabon shugaban kasa ta sauya ra'ayinta kan Ngozi Okonjo-Iweala hanyar ta zama a bude ga 'yar Najeriyar, domin zama mace ta farko daga Afirka da za ta jagoranci kungiyar Ciniki ta Duniya wato (WTO). A karshen watan Oktobar bara, kasashen kungiyar 164 suka kada kuri'ar amincewa da mai shekaru 66 da shida a duniyar, yayin taron da suka gudanar a Geneva.
Sai dai tilas sai manyan daraktocin kungiyar sun amince da ita, kafin wannan zaben da kasashen suka yi mata ya tabbata. Hakan ce ta bai wa tsohon shugaban kasar Amirkan Donald Trump damar dakile nasarar tata. A wancan lokaci, Washington ta bayyana goyon bayanta ne ga 'yar takarar Koriya ta Kudu Yoo Myung Hee, inda ta nunar da cewa Okonjo-Iweala ba ta da kwarewa kan siyasar cinikayya sosai. Duk da cewa 'yar Najeriyar ta mallaki takaddu zama 'yar kasar Amirka tun a shekara ta 2019, hakan bai sa Washington din ta daga mata kafa ba. Bayan da Trump ya fadi zabe, kana 'yar takarar daga Koriya ta Kudu ta janye, a makon da ya gabata, gwamnatin Joe Biden ta sanar da marawa Okonjo-Iweala baya. A dangane da haka, amincewar manyan daraktocin kungiyar na zaman cika sharadi kawai.
Rikicin allurar riga-kafin corona a Afirka ta Kudu
Jaridar die tageszeitung. Jaridar ta ce: Dama tun kafin annobar ta corona, rabin al'ummar kasar ba sa samun kulawar da ta dace a batun kiwon lafiya. Ko yin odar allurar riga-kafin daga kamfanin AstraZeneca mai tarin yawa za ta taimaka? Har yanzu babu tabbas kan yadda hakan zai taimaka wa kayan aikin da suka dade. Da yawan allurar riga-kafi miliyan guda da ta isa kasar a farkon wannan wata na Fabarairu, Afirka ta Kudu na son zama a bar misali ga baki dayan nahiyar. Shugaban kasar Cyril Ramaphosa na son tsarin riga-kafin da ya gabatar a farkon watan Fabarairun da muke ciki, ya kawo mafita ga annobar.
Da yawan wadanda suka mutu sakamakon annobar da ya kai kimanin dubu 46, Afirka ta Kudu na zaman kasar da corona ta fi yi wa illa a baki dayan nahiyar Afirka. Sai dai kuma bincike ya nunar da cewa allurar riga-kafin corona ta kamfanin AstraZeneca na hadin gwiwar Birtaniya da Sweden, da Afirka ta Kudun ta saya daga Indiya, na iya maganin kaso 22 ne kacal na sabuwar kwayar cutar corona da ta bulla a kasar. Da gagarumin tsarin yin riga-kafin, Shugaba Ramaphosa ya bai wa kowa mamaki ganin cewa da ma rabin al'ummar kasarsa ba sa samun isasshiyar kulawa a fannin kiwon lafiya tun ma kafin coronan, kuma ana ganin riga-kafin ba ta kai isa kasashe matalauta ba, cikinsu kuwa har da Afirka ta Kudun da Indiya.
Afirka ta Kudu na yakar rudu
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta nata sharhin ne kan Afirka ta Kudun tana mai cewa nau'i na biyu na kwayar cutar corona na raguwa. Sai dai fargabar ko allurar riga-kafin cutar za ta iya taimakawa na karuwa. Amma akwai sabon fata. A Afirka ta Kudu, bayan katse gudanar da allurar riga-kafi, yanzu akwai sabon yunkuri na sake fara wa. 'Yan kasuwa da 'yan siyasa da kuma masu bincike, na son a hanzarta dawo da yin riga-kafin. A matsayin sabon fatan dai, Afirka ta Kudu za ta yi amfani da riga-kafin kamfanin Johnson & Johnson (J&J), duk da cewa har yanzu ba a kai ga amincewa da ita ba. A hannu guda kuma, kiraye-kiraye na kara yawaita kan kada a yi gaggawar watsar da allurar riga-kafin kamfanin AstraZeneca. Wani binciken kwararru a jami'ar Witwatersrand ta birnin Johannesburg, ya nunar da cewa riga-kafin ta AstraZeneca, na da karfin yakar kananun kwayoyin cututtuka ne kawai.