1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan Afirka

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
October 30, 2020

Zabne shugaban kasa a Tanzaniya da batun huldar diplomasiyya tsakanin Sudan da Isra'ila da ma batun zanga-zangar #EndSATS a Najeriya, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

Tansania Wahlen | Präsident John Magufuli
Shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli Hoto: Ericky Boniphace/AFP

"Tare za mu yaki Shugaba Magufuli," da wannan take ne jaridar Neues Deutschland ta bude labarin da ta rubuta dangane da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da aka gudanar a ranar Laraba  a kasar Tanzaniya da ke gabashin Afirka. Ta ci gaba da cewar, gabanin zaben dai an samu barkewar rigingimu a yankin Zanzibar mai kwarya-kwaryar 'yancin kai. Jam'iyyun adawa dai sun yi taron dangin kokarin ganin karshen gwamnati mai ci. A Tanzaniyar dai sannu a hankali mulkin shugaba John Magufuli ya rikide zuwa na kama-karya, mutumin da ke neman wa'adi na biyu, domin zarcewa kan mukaminsa bayan kammala na farko.

Ina babban jagoran adawar Tsibirin Zanzibar?

Gabanin zaben na ranar 28 ga watan Oktoba dai, an harbe mutane biyar lokacin zanga-zangar nuna adawa da shi. Sabanin sauran yankunan kasar ta Tanzaniya dai, tun a ranar Talata jami'an tsaro da ma'aikatan hukumar zabe suka kada kuri'unsu a tsibirin Zanzibar. Seif Sharif Hamad na jam'iyyar ACT–Wazalendo dai shi ne fitaccen dan takarar adawa a Tsibirin na Zanzibar. Sai dai rahotanni na nuni da cewar an cafke shi a Unguja tsibiri mafi girma a kasar, a daidai lokacin da ya je kada kuri'arsa, a cewar maimagana da yawun jam'iyyar adawar Salim Bimani. Masu lura da lamuran siyasa dai na shakkun sahihancin sakamakon zaben, bayan da aka ayyana shugaba John Magufuli da kasancewa mai rinjaye da mafi yawan kuri'u.
Daga zabe a Tanzaniya sai kuma batun diplomasiyyar sasanta Sudan da Isra'ila. A labarinta mai taken "Dawo da dangantaka amma ta ciki na ciki," jaridar Die Tageszeitung ta ce bayan Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa, Sudan na muradin sabunta dangantaka da Isra'ila, yunkurin da ko a cikin kasar bai samu goyon baya ba. Ta ci gaba da cewa, an dauki watanni ana rade-radi, dab da zaben Amirka sai lokacin ya bayyana. Bayan Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain, Sudan ta yanke hukuncin kulla alaka da Isra'ila a karkashin jagorancin Amirka.

Mayar da hulda tsakanin Sudan da Isra'ilaHoto: Jack Guez/AFP/Getty Images

Ban fishiri in ba ka manda

A cewar shugaba Donald Trump dai, "kasashen biyu na muradin kulla dangantakar zaman lafiya" kuma Sudan da Isra'ilan sun tabbatar da hakan. Sai dai gwamnatin rikon kwarya a Sudan din, ta samu martanin adawa daga al'ummar kasar. Sake mayar da dangantaka da Isra'lar dai na daya daga cikin sharudda biyu da Washington ta gindayawa Sudan din, domin cireta daga jerin kasashen da Amirka a ayyana a matsayin tungar 'yan ta'dda. Tuni dai Khartoum ta cika sharadi daya na biyan kudin diyya na sama da dalar Amirka miliyan 300 ga 'yan uwan Amirkawa da hari ya hada da su a kasashen Kenya da Tanzaniya da Yemen a shekarun 1990s. Cire kasar daga cikin kasashen 'yan ta'adda dai, na nufin Sudan din za ta iya samun tallafin kudi daga ketare.

Zanga-zangar NajeriyaHoto: Temilade Adelaja/Reuters

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung tsokaci ta yi game da ta'azzarar zanga-zangar nan ta adawa da rundunar 'yan sanda da ke yaki da fashi da makami a Tarayyar Najeriya, wato SARS a fadin kasar. Jaridar ta ce hotunan bidiyon da suka mamaye shafukan sada zumunta, na nuna yadda masu gangamin ke gudun neman ceto cikin fargaba.

An dai kafa dokar hana fita a duk jihohin da zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali da kuma fasa rumbunan ajiyar kayan abinci da na masarufi na gwamnati da na daidaikun jama'a ana dibar kaya. A birnin Legas da aka ruwaito mutuwar mutane 12 bayan da jami'an tsaro suka yi kokarin tarwatsa zanga-zangar, an yi fatali da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kafa.