Corona na raguwa a nahiyar Afirka
August 27, 2020Talla
To sai dai babban jami'in na hukumar kula da cututtuka masu yaduwa a Afrika, John Nkengasong ya ce hakan ba yana nufin a koma gidan jiya ba ne domin wannan anobar ba a kai karshenta ba tukuna.
Masu aiko da labarai sun ruwaito jami'in na cewa gwaji da ma hanyoyin kariya da al'umma ke bi ana samun biyan bukata kuma yana da kyau a ci gaba da kiyayewa.
Ya zuwa yanzu kasashen 23 daga cikin 54 a nahiyar Afirka sun sanar da samun raguwar masu kamuwa da cutar. Sama da mutane miliyan daya da dubu dari biyu ne ke dauke da cutar a Afirka wanda rabinsu ke a kasar Afirka ta Kudu.