1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ko Chaina ce kalubalen Amurka a Afirka?

Cai Nebe MTA/LM
January 9, 2025

Chaina ta sake daura damara wajen fadada kawance da kasashen Afirka, tun bayan lokacin da shugaban Amurka mai barin gado Joe Biden ya kai ziyararsa ta farko nahiyar a watan Disambar bara.

Chaina | Afirka |  Wang Yi | Ziyara | Najeriya | Yusuf Maitama Tuggar
Ministan harkokin wajen Chaina Wang Yi da na Najeriya Yusuf Maitama TuggarHoto: Afolabi Sotunde/picture alliance

Tuni dai ministan harkokin wajen Chaina Wang Yi ya fara wata ziyara ta kwanaki uku, a kasashen Namibiya da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da Chadi da kuma Najeriya. Da yake jawabi a Namibiya Mr. Wang ya shaidawa sabuwar shugabar kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah cewa Chaina za ta ci gaba da kasancewa amintacciyar abokiyar hulda da Afrika, domin samar da ci-gaba mai ma'ana. Mai sharhi kan alakar Chainan da Afirka Christian-Geraud Neema ya nunar da cewa, kasashen nahiyar sun fi dogaro da Chaina wajen alakar kasuwanci da samar da ababen more rayuwa da kuma tsaro.

Taron Chaina da AFirka a shekara ta 2024Hoto: Andy Wong/AP/picture alliance

Kokarin mamaye Afirka, ya sanya sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken kai ziyara kasashen Cape Verde da Côte d'Ivoire da Najeriya da kuma Angola a 2024. A shekara ta 2024, Chaina ta shirya taron yaukaka dangantakar kasuwanci mara shinge da kasashen Afirka a birnin Beijing (FOCAC). Zauren taron ya amince Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango shugabantar hadakar kasashen, wanda kuma hakan ke nuna karfin alakar da ke tsakanin Beijing da Kinshasa.

Ghana: Illar cutar Corona ga 'yan kasuwa

02:33

This browser does not support the video element.

Chaina ta  bude sabon babin tallafin dalar Amurka biliyan 51 ga nahiyar, abin da masana irin su Cliff Mboya na Cibiyar Gudanar da Bincike kan Alakar Ghana da Chaina ke cewa akwai sabatta-juyatta dangane da alakar. Lekki a Najeriya da babban titin da ya hade Namibiya da kuma aikin katafaren gidan gona mai amfani da hasken rana da makamashi a Afrika ta Kudu, na daga cikin muhimman ayyukan da Chaina ta assasa a nahiyar.

Tattalin arzikin Chaina na fuskantar barazana a 'yan shekarun baya-bayan nan,to amma bukatar kudi ta sanya ta fadada fukafukanta na cinikayya da kashashe da dama. Ga misali bangaren samar da makamashi ta hanyar amfani da hasken rana, na daya daga cikin bangarorin da Chaina take bukatar abokanan hulda baya ga Amurka da kasashen Turai. Wani babban al'amari da aka kasa fayyacewa shi ne, yadda Afirka da Chaina da Rasha za su yi hadaka wajen cimma manufa guda.