1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Inganta dangantakar Jamus da Afirka

September 12, 2023

Tasirin Turai yana kara raguwa a wasu kasashen Afirka, amma baya-bayan nan Jamus ta fitar da salo a manufofinta na Afirka da ya dogara a kan dabi'un da za su taimaka mata cimma muradunta a nahiyar da duniya ta saka ido.

Jamus | Dakta Bärbel Kofler | Dangantaka | Taron Sauyin Yanayi | Afirka | Kenya
Yar majalisar dokoki kana sakatariya a ma'aikatar kasuwanci da ci-gaban kasa a Jamus Dakta Bärbel KoflerHoto: German Embassy Dhaka

Yayin taron sauyin yanayi na Afirka na farko a birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar Kenya kasashe 54 na Afirka da ke da alhakin kashi hudu cikin 100 na hayakin da ke gurbata muhalli a duniya,sun yi kakkausan suka a kan yin garambawul ga tsarin hada-hadar kudi na duniya tare da yin kira ga kasashen duniya da su goyi bayan kokarin da ake na samar da makamashin da ake iya sabuntawa. Kasashen Duniya da ke Yamma sun ji haka ciki har da Jamus, wadda ta kasance bakuwa a wurin taron.

Karin Bayani: Scholz zai je Afirka kan rikicin Sudan

A wannan karon, gwamnatin Jamus ta zo ba tare da wata shawara ta kanta ba. 'Yar majalisar dokoki kuma sakatariya a ma'aikatar kasuwanci da ci-gaban kasa Bärbel Kofler ta bayyana cewa, ba su da niyyar gabatar da sababbin shirin Jamus a zauren taron duk da yaki da sauyin yanayi babban jigon manufofin harkokin wajen Jamus ne. Wannan furuci dai shi ne martanin gwamnatin Jamus kan sukar da ake yi wa kasar dangane da nuna son kanta, kuma ba ta daukar abokan huldarta na Afirka a matsayin wadanda za su yi tafiya tare.

Mahalarta taron sauyin yanyi na Afirka na farkoHoto: Khalil Senosi/AP/picture alliance

Jami'an diflomasiyya na ganin cewar, Afirka na samun biyan bukatu na zahiri ne kawai daga kasashe kamar Chaina ko Rash a ko kuma Turkiyya, a yayain da idan aka zo kan Jamus za ta cika su ne da jawaban baka. Yakamata Turawa su sani cewa a yanzu Afirka na da zabi, in ji Dokta Paul-Simon Handy na Cibiyar Nazarin Tsaro ta Afirka. A halin yanzu Rasha da Chaina suna taka muhimmiyar rawa a wannan fanni, kasancewar suna bai wa takwarorinsu na Afirka daidai abin da suke bukata.

Karin Bayani:Chaina: Agajin riga-kafin corona ga Afirka

A bangaren Rasha ga misali, tana bayar da taimako yayin da kasar Chaina ta zuba jari mai yawa a fannin samar da ababen more rayuwa a nahiyar. Amma Turai da Amurka saboda yanayin tsarin tattalin arzikinsu mai sarkakiya, na da ka'idoji masu yawa da ke fuskantar jinkiri a kai-a kai. Sai dai irin matakin na Chaina ya zame wa kasa kamar Zambiya babbar matsala, wacce ita ma take fama da dimbin basussuka sakamakon haka. A dangane da haka ne ma Jamus za ta iya yin abin da ya dace a yanzu, ta hanyar saka hannun jari a tsarin zaman lafiyar kasashen kamar yadda manazarta suka nunar.