1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakile 'yancin 'yan jarida a Afirka

May 3, 2022

A kasashen Afirka da dama, 'yan jarida na fuskantar barazana ta kowace fuska mussaman a kasashen Kamaru da Guinea-Bissau da Ruwanda da kuma Mali da ke karkashin mulkin soja.

Hana kafafen yada labarai sakat
A kasashe da dama na duniya musamman Afirka, ana take hakkin 'yan jaridaHoto: Sorapop/Panthermedia/imago images

A galibin kasashen Afirka ana ci gaba da neman hanyoyin da za a tabbatar da 'yancin 'yan jarida, wanda a kullum ke fuskantar barazana. Baya ga barazanar da rayuwar 'yan jaridar ke ciki a kasashe kamar Kamaru, a lokuta da dama wasu 'yan jaridar kan yi batan dabo ko kuma a tsare su na tsawon lokaci. Mancho Bibixy na daga cikin 'yan jaridar Kamaru da har kawo yanzu, babu amo babu labarinsu. Iyalansa har sun cire tsammanin ganin ya sami 'yanci, tun bayan da aka gano maboyarsa a birnin Bamenda da sojojin Kamarun suka killace shi shekaru biyar din da suka gabata. A yanzu haka ya na gidan kaso a birnin Yaounde, inda ya ke zaman wakafi na tsawon shekaru 17. An dai yankewa dan jaridar wannan hukuncin ne, bisa laifukan sabawa shari'a da ma yada labaran karya.

Karin Bayani: Najeriya: Kokarin murkushe 'yan jarida

Da dama dai na ganin dan jaridar na fuskantar wannan hukunci ne, sakamakon ficen da yayi wajen caccakar salon siyasar kasar ta Kamaru a gidan radiyon Abakwa FM da ke yankin masu magana da harshen Turancin Ingilishi a kasar. Ndingana Raymond da ke zama babban mai tace edita labarai a gidan radiyon, ya ce tsare fittaccen dan jaridarya bar babban gibin. 'Yancin gudanar da aikin jarida a kasar ta Kamaru, abu ne mai matukar wahala a shekarun baya-bayan nan. A watan Fabarairun da ya gabata kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Internetional, ta rubutawa shugaban kasar Paul Biya wasika domin yi masa tambayoyi kan abun da ta ce tsare 'yan jarida ne ba bisa ka'ida ba. Kungiyar ta ce, akwai kimanin 'yan jarida hudu da ke yankin da ake magana da harshen Turancin Ingilishi a gidajen yari.Tsi Conrad kamar Mancho Bibixy na zaman gidan wakafi na shekaru 15, bayan da aka yanke masa hukunci a shekarar 2018 bisa laifin sukar lamirin gwamnati. Tamfu Christopher wanda na hannun daman Conrad ne, ya ce hukumomin sun kama aminin nasa saboda yi wa sauran takwarorinsa 'yan jarida barazana, tare da fakewa da sabuwar dokar da gwamnati ta fitar a yaki da ta'addanci domin musgunawa manema labarai. A kasar Mali da ke karkashin mulkin soja bayan juyin mulkin da aka yi, aikin jarida na fuskantar babbar barazana. Gwamnatin mulkin sojan ta Mali dai, yi na dakatar da kafafen yada labarai biyu, a kasar da ke zama mallakin kasar Faransa.

Tanzaniya na zaman guda daga cikin kasashen da ake take hakkin 'yan jarida a AfirkaHoto: Article19-East Africa

Karin Bayani: Shin fadin albarkacin baki ya zama laifi karkashin Shugaba Akufo-Addo na Ghana?

A Guinea-Bissau kuwa a baya-bayan nan sai da gwamnatin kasar ta rufe fiye da gidajen radiyo 70 saboda rashin biyan kudin sabunta lasisinsu, sai dai kuma wasu sun biya kudin da dadewa amma kuma kuma ba sa watsa shirye-shirye saboda suna jiran ma'aikatar sadarwar kasar ta gama tantance kayayyakin aikinsu domin ganin ko ya yi daidai da lasisin nasu. Wannan batu dai, wasu na yi masa kallo na bambarakwai. Haka batun yake dangane da yadda aikin jarida ke tattare da tarin kalubale, a kasashe kamar Afirka ta Kudu da Zimbabuwe da Ghana da ma sauran kasashen Afirka.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani