Rawar Afirka a yakin Ukraine
June 16, 2023Talla
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da wasu shugabannin kasashen Afirka sun isa Ukraine din ne a wannan Juma'ar (16.6.2023) don ganawa da shugaban kasar Volodymyr Zelenskyy da farko, kafin daga bisani su tattauna da shugaba Vladimir Putin a birnin St Petersburg a gobe Asabar.
Suna fatan karfafa gwiwar shugabannin Ukraine da na Rasha su amince da tsarin tattaunawar da diflomasiyya ke jagoranta.
Tawagar ta shugaba Ramaphosa ta kunshi Macky Sall na Senegal da Hakainde Hichilema na Zambiya da kuma shugaban Comoro Azali Assoumani, wanda a halin yanzu ya ke jagorantar kungiyar Tarayyar Afirka, daura da manyan 'yan siyasar kasashen Yuganda da Masar da kuma Kwango.