Afirka ta Kudu: An kame 'yan kasashen waje
November 16, 2019![Südafrika Kapstadt | Außeinandersetzungen zwischen Polizisten und Füchtlingen während Protesten vor UN Flüchtlingshilfe](https://static.dw.com/image/51055473_800.webp)
Tun da farko daruruwan masu neman mafaka sun afka harabar cibiyar ne da nufin cigaba da wani zaman dirshan din da suka fara tun ranar 8 ga watan Oktoban da ya gabata, inda suka bukaci cibiyar ta mayar dasu wasu kasashen don tsira da rayukan su, biyo bayan rikicin kyamar bakin da ya afku a kasar a watan Satumba inda batagari a Afrika ta Kudu suka dinga kisa da kone baki tare da washe musu dukiyoyi.
A ranar Juma'ar da ta gabata hukumar 'yan gudun hijirar ta Majalisar Dinkin Dunya a Afirka ta Kudu ta bayyana cewar ba za ta tuhumi 'yan kasashen ketare da laifin cin zarafin wani jagoran addinin Kirista a cocin Cape Town ba, kasancewar 'yan kasashen ketaren na zaune ne a cocin da yake shugabanta saboda tserewa daga farmakin masu kyamar baki, duk kuwa da cewa Afirka ta Kudu na alfaharin samarwa baki shaidar zama a kasar tare da ayyukan yi cikin sauki.