1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'a kan zargin da ake wa Zuma

Binta Aliyu Zurmi LMJ
July 19, 2021

An koma zaman shari'ar tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma. Ana dai  zargin Zuma da yin sama da fadi da dukiyar kasa, a lokacin mulkinsa.

Südafrika | Jacob Zuma
Hoto: Shiraaz Mohamed/AP Photo/picture alliance

Ana wannan zaman kotu ne ta kafar bidiyo, sai dai lauyan da ke kare tsohon shugaban kasar ta Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya nemi a dage zaman, domin ya samu damar halartar kotun a nan gaba. Duka wannan na zuwa ne bayan da Zuma ya kwashe sama da mako guda a gidan yari bisa laifin raina kotu da ya yi, lamarin da ya janyo gagarumar tarzoma a kasar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200 da jikkata wasu da dama, baya ga kone gine-ginen gwamnati da na al'umma gami da wasoson dukiya.