Afirka ta Kudu: Ma'aikatan hakar zinari 4 sun mutu
May 4, 2018Talla
James Wellsted, mai magana da yawun kamfanin ya ce akwai wasu uku da suka makale a karkashin kasa, a yayin da aka yi nasarar zakulo shida da tuni aka ruga da su asibiti don basu kulawa, girgizar kasa mai karfin maki biyu da digo biyu a ma'aunin rishta, ta auku ne a wannan Juma'a inji sanarwar kamfanin.
Tuni kungiyar ma'aikatan ma'adinai ta kasar NUM ta baiyana bacin ranta kan yawaitar hadura da ke lakume rayukan ma'aikata a kamfanin na Sibanye-Stillwater, don ko a watan Febrairu ma, kusan masu hako ma'adinai dubu daya ne suka makale a yayin aiki bayan matsalar katsewar wutar lantarki a ma'aikatar, kwanaki biyu bayan wannan wasu biyu suka mutu bayan ruftawar kasa a wata ma'aikatar hakar ma'adinai mallakar kamfanin.