Afirka ta Kudu na zargin jami'an 'yan sanda da cin hanci
April 24, 2026
Talla
A ranar Talata ne dai Fannie Masemola ya bayyana a kotu, kuma an shirya komawa kotun tare da wasu manyan jami'an 'yan sanda 12 da ake zargi da zamba, da cin hanci da rashawa da kuma halasta kudaden haram dangane da kwangilar, wadda ake zargin an bai wa wani kamfani na cikin gida ba bisa ka'ida ba.
Tuhumar da ake yi wa Masemola na da nasaba da kujerarsa a matsayin babban jami'in da ya kamata ya kula da dukiyar hukumar 'yan sanda.
Tuni Shugaba Cyril Ramaphosa ya nada Puleng Dimpane, kwamishinan kula da harkokin kudi a hukumar, a matsayin mukaddashin babban jami'in 'yan sanda, yayin da Masemola ke fuskantar shari'a.