Kotun ICC ta soma fuskantar kalubale daga Afirka
October 21, 2016Wannan mataki dai na Afirka ta Kudu na ficewa daga Kotun ta kasa da kasa, na a matsayin wani babban kalubale ga kotun mai cibiya a birnin Hague na kasar Holland. Kamar yadda aka tanadi tsarin ficewar, hukumomin na Pretoria sun sanar wa babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya wannan mataki na su a rubuce, a cewar ministan harkokin wajen kasar ta Afirka ta Kudu Michael Masutha.
A shekara ta 2003 ne dai kotun ta kasa da kasa ta ICC ta soma aikinta wadda kuma ke a matsayin kotun farko da aka kafa da ke bin diddigin masu aikata manyan laifuka musamman ma na yaki, a inda ake aiwatar da kashe-kashen mutane barkatai.
Sai dai daga cikin bincike goma da kutun ta kaddamar, guda takwas dukannin sun shafi kasashen Afirka ne kwai, inda a baya ma kungiyar Tarayyar Afirka ta soki lamirin wannan mataki na nuna banbanci da kotun ke yi a cewarta.