1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka ta Kudu ta kama mai adawa da mulkin Jamhuriyar Benin

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 16, 2026

Kemi Seba 'dan asalin Benin, ya yi kaurin suna wajen adawa da Faransa da ma shugabannin Afirka masu dasawa da ita.

'Dan gwagwarmaya Kemi Seba mai adawa da gwamnatin Jamhuriyar Benin, wanda 'yan sanda suka kama a Afirka ta Kudu
'Dan gwagwarmaya Kemi Seba mai adawa da gwamnatin Jamhuriyar Benin, wanda 'yan sanda suka kama a Afirka ta KuduHoto: Komsomolskaya Pravda/Picvario/picture alliance

'Yan sandan Afirka ta Kudu sun kama 'dan rajin yaki da manufofin kasashen yamma Kemi Seba, wanda Jamhuriyar Benin ke nema ruwa a jallo, bisa zargin goyon bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, cikin watan Disamban 2025, tare da tunzura jama'a bijirewa gwamnati.

Tuni 'yan sandan suka fara shirye-shiryen mayar da shi kasarsa ta asali Benin, tare da 'dansa, don fuskantar shari'a, kamar yadda suka sanar a wannan Alhamis.

Karin bayani: Kemi Seba zai tsaya takara a Benin

Seba, wanda sunansa na asali shi ne Stellio Gilles Robert Capo Chichi, ya yi kaurin suna wajen adawa da Faransa da ma shugabannin Afirka masu dasawa da ita, haka zalika shi ne jagoran wata kungiya mai zaman kanta, wadda ke rajin kishin muradan Afirka zalla.

Karin bayani: Dan takaran gwamnati ya lashe zabe a Jamhuriyar Benin

An kama shi ne tare da dansa mai shekaru 18, lokacin da suka je sayayya wani shago a birnin Pretoria ranar Litinin, tare da wani mutum da ake zargi da kulla kutunguilar shigar da su Zimbabwe ba bisa ka'ida ba, a kokarinsu na tsallekewa zuwa Turai.

Karin bayani:Sabuwar gwamnatin Jamhuriyar Benin da hulda da makwabta?

A shekarar 2024, Faransa ta soke izinin zama 'dan kasa na Seba da aka haifa a kasar, sakamakon yadda ya fito fili karara, ya nuna goyon bayansa ga yunkurin juyin mulki a kasarsa ta asali Benin, wanda yake da mabiya miliyan daya da rabi a shafin sada zumunta.