Afirka ta Kudu ta nemi dawo da mutanenta da ke yakin Rasha
February 10, 2026
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu ya tattauna da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a wannan Talata, game da yadda za a mayar da sauran 'yan Afirka ta Kudu gida daga Rasha, bayan sanya su cikin sojojin Rasha da ke yakar Ukraine.
Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar, ta ce Mr Ramaphosa ya sha alwashin cimma wannan muradi na mayar da 'yan kasarsa gida, bayan yaudararsu da aka yi a matsayin sojojin haya.
A cikin watan Nuwamban 2025 ne wasu 'yan Afirka ta Kudu 17, suka nemi daukin mahukuntan kasarsu, domin ceto daga mawuyacin hali da suka samu kansu a ciki a kasar Rasha.
Karin bayani : Afirka ta Kudu ta nemi dawo da mutanenta da ke yakin Rasha
A watan na Nuwamba ne, ministan harkokin wajen Ukraine ya yi ikirarin cewa sun gano sojojin haya sama da 1,400 a cikin rundunar sojin Rasha, wadanda suka fito daga kasashe 36 na Afirka.
A wani labarin kuma Kenya ta sanar da shirinta na aike wa da ministan harkokin wajenta zuwa Rasha, domin neman ba'asi kan yawaitar samun rahoton mutuwar 'yan kasarta da aka tilasta wa shiga yakin Rasha da Ukraine, yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka.
Ministan harkokin wajen Kenya Musalia Mudavadi, ya sanar a wannan Talata cewa zai kai ziyara Moscow, domin lalubo hanyar yi wa tufkar hanci, kan wannan batu mai tayar da hankali.
Mr Mudavadi ya bayyana cewa 'yan Kenya fiye da 30 aka ceto daga Rasha, a cikin watanni biyu da suka gabata, kuma an tarwatsa wani gungun 'yan yaudara da ke shirya tafiye-tafiye zuwa Rasha.
Kenya ta yi tur da yadda ake hilatar 'yan kasarta da alkawarin samun ayyuka masu gwabi, to amma ga mamakinsu sai su wayi gari da ganinsu a filin daga, lamarin da ke jefa rayuwarsu cikin hadarin gaske.