1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka ta Kudu ta jinkirta tafiya gasar cin kofin duniya

May 31, 2026

Jinkirin na da nasaba da matsalolin da wasu daga cikin 'yan wasa da jami'an tawagar kwallo kafar suka fusakanta wajen samun biza.

WM 2026 Qualifikation Südafrika vs Ruanda
Hoto: Julius Ntare/empics/picture alliance

Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu ta sanar da cewa matsalar samun biza ta sa an jinkirta tafiyar tawagar 'yan wasan kasar zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026, wadda za a fara daga ranar 11 ga watan Juni a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Tawagar 'yan wasan da ake wa lakabi da 'Bafana Bafana', ta shirya tashi daga birnin Johannesburg a ranar Lahadi cikin jirgin haya zuwa Mexico domin fara atisaye, sai dai a cikin wata sanarwa, hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu ta ce wasu daga cikin 'yan wasa da jami'an tawagar sun fuskanci matsaloli wajen samun biza, lamarin da ya hana tafiyar kamar yadda aka tsara.

Har yanzu dai ba a bayyana adadin mutanen da ba su samu bizar ba, amma tashar talabijin din gwamnatin Afirka ta Kudu SABC, ta ruwaito cewa akalla mutum 20 daga cikin tawagar har yanzu na jiran a kammala aikin ba su biza a ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Johannesburg.

A gasar ta bana dai, Afirka ta Kudu na a cikin rukuni A, wanda ya kunshi kasashen Mexico mai masaukin baki, da Jamhuriyar Czech da kuma Koriya ta Kudu.