1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ramaphosa ya nuna rashin jin dadinsu

Zainab Mohammed Abubakar
November 29, 2021

Shugaba Cyril Ramaphosa ya nemi kasashe da su soke matakinsu na haramta zirga zirgar jirage daga yankinsa biyo bayan bullar sabon nau'in coronavirus watau Omicron.

Deutschland | G20 | Compact with Africa meeting in Berlin | Cyril Ramaphosa
Hoto: Tobias Schwarz/REUTERS

Gomman kasashen nahiyar Turai da Asiya ne dai suka sanya Afrika ta Kudun da makwabtanta cikin jerin kasashen masu hatsarin zuwa, tun bayan da masana kimiyya suka bayyana bullar Omicron a ranar 25 ga watan da muke ciki na Nuwamba.

Matakin dakatar da tafiye tafiyen jiragen saman dai, ya bata wa shugabannin kasashen Afirka rai. A jawabinsa na farko kusan mako guda bayan bullar sabon nau'in Omicron, shugaba Ramaphosa ya bukaci kasashen da su gaggauta janye wannan matakin ba tare da bata lokaci ba.

Hukumar lafiya ta duniya dai ta ayyana nau'in Omicron din a matsayin abun damuwa, a yayin da kwararru a fannin kimiyya ke ci gaba nazarinsa.