1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka ta Kudu: 'Yar Jacob Zuma ta yi murabus daga majalisa

Mouhamadou Awal Balarabe
November 28, 2025

Ana zargin Duduzile Zuma-Sambudla da dibar 'yan kasar Afirka ta Kudu aikin tsaro don su yi wa Rasha yaki a kasar Ukraine. Amma ta yi alkawarin ba da cikakken hadin kai ga bincikenda ake gudanarwa.

Duduzile Zuma-Sambudla, gabanin shari'a a Durban kan tuhumar ta da tarzoma
Duduzile Zuma-Sambudla, gabanin shari'a a Durban kan tuhumar ta da tarzoma Hoto: AP Photo/picture alliance

'Yar tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ta yi murabus daga majalisar dokoki sakamakon zarginta da ake da dibar 'yan kasa aikin tsaro don su yi wa Rasha yaki a kasar Ukraine. A wani taron maneman labarai da ya gudanar a birnin Durban, darektan jam'iyyar MK da mahaifinta ya kafa, ya sanar cewar Duduzile Zuma-Sambudla za ta ba da cikakken hadin kai ga binciken da hukumomin da abin ya shafa ke gudanarwa.

Duduzile Zuma-Sambudla da mahaifinta Jacob Zuma da suka halarci taron manema labarai ba su yi wani jawabi. Amma 'yar uwarta ta zarge ta a makon da ya gabata da marar hannu a daukar 'yan Afirka ta Kudu 17 aikin tsaro, wadanda suka yi kira ga Shugaba Cyril Ramaphosa da ya fitar da su daga halin da suke cikia a yankin Donbas na Ukraine.

Karin bayani: Zaben Afrika ta Kudu: Zuma ya daukaka kara

Fadar mulki ta Kyiv ta ba da rahoton cewa an gano mayaka 1.426 da suka fito daga kasashen Afirka 36 a cikin jerin bakin da Rasha ke amfani da su a fagen yaki a Ukraine.

 An zabi Duduzile Zuma-Sambudla a majalisar dokokin Afirka ta Kudu ne a watan Yunin 2024, amma tana fuskantar tuhumar tayar da tarzomar da ta barke bayan da aka kama mahaifinta saboda kin bayar da shaida a shari'ar cin hanci da rashawa da ake yi masa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 350.