Afirka ta soki na'am da Isra'ila ta yi da Somaliland
December 27, 2025
Talla
Yankin Somaliland dai ya ayyana ballewa daga Somaliya ne a shekarar 1991, amma ba wata kasar duniya da ta taba amincewa da ita sai a jiya Juma'a.
Shugaban Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya ce duk wani yunkuri da zai raunana ikon mallakar Somaliya, na iya barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar.
A jiya Juma'ar, gwamnatin Somalia ta yi watsi da matakin Isra'ila, tana kiran sa ba bisa ka’ida ba, tare da jaddada cewa yankin arewa har yanzu ɓangare ne na cikakken ikon Somalia.
A halin da ake ciki kuma, kungiyar mayakan Al-Shabab, wadda ke da alaka da Al-Qa’ida, ta sha alwashin yin yaƙi da duk wani yunkuri na Isra’ila na ikirari ko amfani da wani ɓangare na Somaliland bayan wannan amincewa.