Afirka ta Tsakiya ta amince da kudin Bitcoin
May 6, 2022Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ce kasa ta farko a yankin Tsakiyar Afirkada ta amince da fara amfani da kudin Intanet na Bitcoin a hukumance. Majalisar dokokin kasar ta amince da kudin na Bitcoin cikin gaggawa duk da fargabar da wasu a kasar ke nunawa game da rashin tabbas a bangaren hadari da ake gani a game da kudin a duniya.
Gwamnatin Shugaba Faustin Touadera wadda ta amince da amfani da kudaden Intanet din a hukumance a matsayin kudin kasa, ta ce tana da yakinin shigo da kudin a tsarin hada-hada ta kasar da zai inganta rayuwar al’umma.
Haka ma yin hakan a cewar gwamnatin zai sanya kasar cikin jerin kasashen da suka yi kukan kura a taswirar duniya wajen amincewa da kudaden na Bitcoin duk da dari-dari da ake yi da su. Masharhanta kan lamuran siyasa da masana harkokin kudade na ci gaba da gargadi kan gaggawar amince da kudaden a kasa, inda suke cewa ba zai taba iya warware matsalolin kasa-da-kasa ba.
Duk da arzikin zinare da lu’u-Lu’u da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke da shi, kasar na ci gaba da zama cikin jerin kasashe matalauta a duniya, da kuma ke fama da rikice-rikice na tsawon shekaru.
A yanzu kasar na amfani ne da kudaden CFA da Faransa da ta rene ta ta bar mata. Wasu na ganin amincewa da Bitcoin da kasar ta yi, a matsayin wani kokarin da kasar Rasha ke yi na rusa darajar kudin na CFA na Faransa, domin ta samu iko da tattalin arzikin kasar.
Darajar kudaden na Bitcoin a bara ta yi wani irin tashi da ya kamar kashi 150%, da ya kai na miliyoyin dala. Sai dai kuma sun sake faduwa a watannin baya-bayan nan daga bayanan alkaluman hada-hada na ranar Larabar da ta gabata.