Afirka: Shirin kula da lafiya da fasahar AI
January 21, 2026
Talla
Hadin gwiwar, mai suna Horizon1000, yana shirin yin aiki tare da shugabannin Afirka don gano yadda za a yi amfani da fasahar, shirin da ake saran kaddamar da shi a kasar Ruwanda.
Bill Gates a shafinsa na yanar gizo ya ce, a kasashe da ke fama da talauci da karancin ma'aikatan lafiya daura da rashin kayayyakin more rayuwa na tsarin kiwon lafiya, fasahar kirkira ta AI na iya zama abin da zai canza yanayin fadada samun damar samun kulawa mai inganci .
Gidauniyar ta riga ta kafa wasu shirye-shirye na fasahar AI, yayin da Ruwanda a bara ta kafa cibiyar kiwon lafiya ta AIa Kigali.