Afrika ta Tsakiya ta bukaci taimakon MDD
September 22, 2017Talla
Shugaba Touadera ya mika kokon baransa ga Majalisar a yayin da yake gabatar da jawabinsa a taron Majalisar da ke gudana a birnin New York na kasar Amurka. Shugaban ya ce Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na cikin wani hali inda take fuskantar barazanar tsaro daga kungiyoyi na masu tayar da kayar baya, kafin ya kuma yi kira ga majalisar na taimaka mata da kayayyakin agaji ga miliyoyin mutane da yaki ya daidaita.
Mutane fiye da dubu dari shida ne suka rasa matsuguni a rikicin da ya biyo bayan tunbuke tsohon shugaba Francois Bozize baya ga wasu sama da dubu dari biyar da suke gudun hijra yanzu haka a wasu kasashe da ke makwabtaka da kasar.