1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Zuri'ar Afrikaners za su koma Amurka daga Afirka ta Kudu

Abdourahamane Hassane
May 9, 2025

Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewa, a cikin kwanaki masu zuwa Amurka za ta karbi rukunin farko na Afrikaners, zuri'ar Turawa mazauna Afirka ta Kudu, wadanda ta bai wa mafaka ta 'yan gudun hijira.

Hoto: DW/V.da Rocha

Donald Trump ya zargi mahukuntan  Afirka ta Kudu da muzgunawa wadannan fararen fata 'yan tsiraru na Afrikaner, lamarin da gwamnatin Pretoria ta musanta.

Kafofin yada labarai na New York Times, sun  ambaton majiyoyin  da ke ba da rahoton cewar gwamnatin Amurka na shirin yin maraba da wasu 'yan Afrikaners da dama zuwa Amurka tun daga ranar Litinin, mai zuwa.

Afrikaners da suka fito daga  kasar Holland wadanda suka isa yankin kudancin  Afirka  fiye da karni uku da suka gabata, su ne mafi yawan fararen fata na Afirka ta Kudu kashi 7.3%. cikin dari.