Agadez: Takaddamar rushe gidaje fiye da 700
October 15, 2025
Talla
Gidaje sama da 700 aka ce za a rushe a cikin birnin Agadez, gidajen da hukuma ta ce suna zaune ba kan ka'ida ba domin sun shiga cikin filin ASECNA. Kamfani mai kula da zirga zirga jiragen sama a Afirka da Madagascar, inda hukuma ta bai kwamitin wa'adi zuwa 15 ga watan oktoba da ake da niyar rushe gidajen, abinda ya sa kwamitin masu gidajen daukar lauya don a kwatar musu da hakkinsu.
Wannan rusau zai shafi dubban mutane da suka share shekaru masu yawa suna zaune a wannan wurin, inda bayan gidaje akwai wurare da jama'a suke neman abinci.