1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Agajin Jamus a wasu kasashen Afirka ta Yamma

April 13, 2023

Tawagar ministocin Jamus ta kammala ziyarar da ta kai Nijar da Mali. Huldar diflomasiyyar shekaru 62 da batun tsaro da raya kasa da na jin kai sun dauki hankali a ziyarar.

Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius yayin ziyara a Nijar
Ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius yayin ziyara a NijarHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

A Jamhuriyar Nijar wata tawagar ministocin Jamus ta kammala ziyarar aiki da ta kai a kasar a wani rangadi da ta hada kasashen Nijar da Mali. Batun huldar diflomasiyyar da ta hada kasashen biyu yau shekaru 62 da kuma maganar tsaro da ta taimakon raya kasa da na jin kai na daga cikin muhimman batutuwan da tawagar jami'an Jamus din ta tattauna da mahukuntan kasar ta Nijar.

Tawagar jami'an gwamnatin kasar ta Jamus karkashin jagorancin ministar kula da tattalin arziki Svenja Schulze da ministan tsaro Boris Pistorius, ta soma ne da ziyaratar wani sansanin sojan Jamus a birnin Yamai da kuma rumbun ajiyar kayan abincin agaji na hukumar kula da samar da abinci ta Majalisar DinkinDuniya wato PAM, kana ta karkare da ofishin ministan harkokin wajen Nijar. Da take jawabi a gaban manema labarai ministar Jamus, Svenja Schulze ta fara ne da yin waiwaye kan aikin da Jamus ta yi a Nijar a tsawon shekaru 62 na huldar da ta hada kasashen biyu.

Ta ce ''Nijar kasa ce wacce muke da hulda ta aminci da yarda da ita, kana kasancewarta abar misali a bangaren zaman lafiya a yankin. Bana mun yi bikin shekaru 60 na hulda tsakanin kasashen biyu. A tsawon wadannan shekaru, Jamus ta zuba kudi miliyan dubu da 260 na Euro a Nijar, wanda ya taimaka ga inganta rayuwar mutane kimanin dubu 450. Mun gina ajujuwa sama da 400 inda ake karantar da yara, kana mata sama da miliyan daya ke cin moriyar gudunmawarmu a fannin kiwon lafiya''

Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Daga nashi bangare Ministan tsaron kasar Jamus, Boris Pistorius bayani ya yi kan rawar da Jamus ke takawa wajen tallafa wa Nijar a fannin tsaro.

Ya ce ''a wurinmu, Nijar na matsayin kasa mafi tabbas a yankin. Muna da kyakkyawar hulda a fannin harkokin soja. Ko a yanzu na ziyarci wajen da ake aiwatar da wani shiri na horas da sojojin Nijar.  Amma kuma mun ga akwai bukatar taimakawa a fannin farar hula, dalilin da ya sa muke ci gaba da aiki tare. Domin duk ci gaban da aka samu a wannan yanki da juriyar da talakawa ke nunawa kan matsalolin da suke fuskanta na iya rugujewa. Don haka akwai bukatar kara tabbatar da tsaro a kasar da ma yankin. Kuma wannan aiki ne da gwamnatin Jamus ta dukufa a kansa''

Baya ga bitar tallafin da Jamus ke bai wa Nijar, ko a wannan karo tawagar jami'an gwamnatin kasar ta Nijar ba ta zo hannu rabbana ba a cewar mai masaukin baki ministan harkokin wajen Nijar, Malam Hassoumi Massaoudou.