1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ahmed Musa zai iya kawo sauyi a Kano Pillars?

Nasir Salisu Zango ZMA
July 9, 2025

Masana wasanni na yin martani dangane da nada kaftin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Ahmed Musa a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwa ta Kano Pillars.

Hoto: Reuters/T. Hanai

Masana a fannin wasanni na yin martani dangane da nada kaftin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Ahmed Musa a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwa ta Kano Pillars, matakin da ake ganin zai iya farfado da martabar kungiyar yayin da wasu masu fashin baki ke cewar sai an yi hattara domin taura biyu bata taunuwa.

Tun bayan da ya rasa kulob a kasashen waje Ahmed Musa ya dawo gida inda ya sanya wa kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars riga a matsayin dan wasanta, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu la'akari da irin gagarumar gudunmawar da dan kwallon ya baiwa kungiyar har ta kare a matsayin ba-yabo ba-fallasa a kakar wasanni da ta gabata.

Hoto: Getty Images/AFP/P. Desmazes

Kwatsam kuma sai aka jiyo sanarwar cewar gwamnatin Kano ta nada Ahmed Musa a matsayin sabon shugaban kungiyar kacokan, matsayin da Ahmed din ya lashi takobin rikewa bilhakki ya na mai shan alwashin yin duk me yiwuwa wajen aiki da dukkan kusoshin kungiyar da zummar daga darajar ta.

To amma masana masu fashin baki kan harkokin wasanni irin su Muhmmad Sani Uba na ganin cewar nadin Ahmed Musa abin marhabin ne, amma kasantuwarsa dan wasa kuma shugaban kungiya zai iya dakushe kokarinsa kasancewar taura biyu bata taunuwa a baki daya.

To amma Bashir Hayatu Jantile masanin harkokin wasanni na da ra'ayin cewar, babu laifi idan Ahmed Musa ya zama shugaba kuma dan kwallo domin ba kansa ne farau ba.

Sh ikuwa mai magana da yawun kungiyar ta Kano pillars Ismaila Tangalashi cewa yayi, an musu goma ta arziki wajen kawo Ahmed Musa bisa wannan mukami

Abin da ya rage dai shi ne sauyin da za a gani na wannan sabon nadi wanda sai dai a jira kankamar kakar wasanni ta bana.