Ahmedinejad na fara wata ziyarar aiki ta yini biyu a Saudiyya
March 3, 2007Talla
A yau asabar shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad ke fara wata ziyarar aiki ta yini biyu a kasar Saudiyya. Wata sanarwa daga gwamnatin birnin Teheran ta ce ziyarar wadda ta ke ta farko da Ahmedi Nijad zai kaiwa shugabannin kasar ta Saudiyya, zata ba da damar shawartawa akan halin da ake ciki a yankin GTT. Manazarta na ganin ziyarar tamkar wani abin al´ajabi musamman kasancewar Saudiyya babbar kawar Amirka ce. Hakazalika zubar da jinin juna da ake yi tsakanin mabiya darikun Sunni da Shi´a a Iraqi ta sa Iran da Saudiyya na yiwa juna kallon hadarin kaji.