1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin agazawa masu tsananin bukata a Siriya na samun nasara

February 13, 2014

Gwamnatin Siriya ta tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta, domin ci gaba da kai agaji a birnin Homs, wanda dakarun gwamnatin ke yi wa kawanya.

Krieg in Syrien Rotes Kreuz Evakuierung in Homs 10.02.2014
Hoto: Str/AFP/Getty Images

Gwamnan birnin Homs, Talal al-Barazi, ya bayyana cewar farawa daga wannan Alhamis (13. 02. 14) ne gwamnati ta tsawaita wa'adin yarjejeniyar tsagaita bude wuta, domin samun sukunin kai agaji ga karin fararen hular da ke cikin ukuba a cikin birnin.

Ya kuma kara da cewar, ya zuwa yanzu kimanin mutane dubu 1,400 ne suka yi nasarar ficewa daga birnin a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wutar da Majalisar Dinkin Duniya ta cimma tare da bangarorin da ke cikin rikicin na Siriya tun daga ranar Jumma'ar da ta gabata (07.02.14).

Sai dai kuma gwamnan na Homs, ya ce akwai wasu mutane 220 wadanda hukumomi ke kokarin tantancesu gabannin basu damar ficewa daga birnin, bayan amsa wasu tambayoyin da jami'ai ke yi musu.

Hoto: Reuters

Agaji ga mabukata a birnin Homs

Matakin tsawaita wa'adin na kwanaki uku kuwa ya zo ne jim kadan bayan da jami'ar da ke aiki da Hukumar kula da 'yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Melissa Fleming ke cewar, burin da suke son cimma shi ne taimakawa wadanda ke cikin matsanancin hali:

Ta ce "Muna yin iya kokarinmu domin kai agaji ga wadanda ke fama da matsala, game da sanya ido da kuma samar da kayayyakin agaji ga mabukata ba tare da nuna son kai ga wani bangare ba."

Ita ma Hukumar kula da Lafiya ta Duniya WHO ta ce ta himmatu ga kulawa da wadanda suka sami rauni a birnin na Homs, sakamakon killacewar da dakarun na gwamnatin suka dade suna yi a birnin, kamar yadda jami'a a hukumar, Fadela Chaib ta fadi:

Ta ce "Akwai majiyyata da dama, wadanda basu sami cikakkiyar kulawa ba a birnin Homs, kasancewa akwai asibiti daya tilo ne da ya cika makil da marasa lafiya a birnin, wanda kuma ke fama da karancin kayan aiki da ma'aikatan lafiya."

Sai dai kuma aikin bayar da agaji na tafiya ne a dai dai lokacin da sassan da dakarun gwamnatin Siriya tare da 'yan tawayen ke ci gaba da fafatawa a wasu yankunan kasar, inda hatta a wannan Larabar ma, Kungiyar kare hakkin bil'Adama ta kasar Siriya wadda ke da cibiya a Birtaniya ta bayyana cewar, akalla mutane 51 ne suka mutu sakamakon fada a birnin Aleppo.

Lakhdar BrahimiHoto: Imago/Xinhua

Cikas a taron warware rikicin Siriya

Can a birnin Geneva na kasar Switzerland kuwa, babban mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya a rikicin na Siriya Lakhar Brahimi ne ke fafutukar ceto tattaunawar samar da zaman lafiya daga rugujewa, bayan da kawancen 'yan adawar suka gabatar da wani daftarin da ke kunshe da bukatunsu, kamar yanda kakakin kawancen Louay Safi ya yi karin haske:

Ya ce" Muhimman batutuwan da daftarin ya tabo dai su ne samar da gwamnatin wucin gadin da za ta kula da batun tsagaita bude wuta, da tabbatar da bin doka da oda, game da kokarin sasanta tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna a Siriya."

Sai dai kuma a nasu bangaren, wakilan gwamnatin Siriya, sun ma ki tattauna batun, inda a maimakon haka, suka bukaci sanya batun yakar wadanda ta kira 'yan ta'adda a sahun farko.

Ta fuskar diflomasiya kuwa, wani daftarin da Rasha ta gabatar wa Majalisar Dinkin Duniya ne ya sami goyon bayan kasashen yammacin duniya da na Larabawa dangane da kai agaji zuwa Siriya, amma kuma wanda Rashar ta ce bai kunshi sanyawa mahukunta a Siriya takunkumi ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu