1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iNajeriya

Aikin ceto na tafiyar hawainiya a Maiduguri bayan ambaliya

September 11, 2024

Dubban mutane sun makale a gidajensu yayin da ake kasa ciro gawawwakin wadanda suka mutu, a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan tserewar wasu namun daji. Amma gwamnatin Najeriya ta ce za ta saukaka matsalar jin kai.

Ambaliya ta yi barna a Maiduguri, amma ruwan da ke malala ya fara raguwa
Ambaliya ta yi barna a Maiduguri, amma ruwan da ke malala ya fara raguwaHoto: Musa Ajit Borno/AP/dpa/picture alliance

Ruwan da ke malala a cikin unuwannin Maiduguri ya fara raguwa, lamarin da ya sa wasu fara shiga gidajensu don duba irin barnar da ambaliya ta yi. Amma a wasu wuraren, har yanzu ruwan na ci gaba da malala, inda ake ganin rufin kwanon gidaje kawai. Hukumomi da sauran kungiyoyin agajin na shiga sako-sako suna kokarin fito da mutane da suka makale a muhallansu.

Karin bayani: Ambaliya ta kashe mutane a Najeriya

Jami'an NEMA na kai wa wadanda ambaliya ta shafa agajin gaggawa a MaiduguriHoto: AUDU MARTE/AFP

A'isha Abba Grema ta Kungiyar Grassroot Mobilizers for better Nigeria initiative , daya daga cikin masu gudanar da ayyukan jin kai ta ce suna kokarin kai dauki ga mabukata. Jami'ar ta ce: "Muna da masu ceto da suke shiga, muna da wadanda suka iya ruwa, su ne ke shiga ruwan su fito da tsofaffi da mata.... Mun cire wadanda za mu iya cirewa kuma yanzu haka muna da motoci da suke kai agaji na abinci da kuma kwashe mutane daga wurare da suka makale.....”

Mutane da dama sun tagayyara sakamakon ambaliya

Sai dai har yanzu akwai wuraren da ruwa bai gama janyewa ba, duk da cewa ya ragu idan aka kwatanta da ranar da aka fara ambaliya a Maiduguri sakamakon ballewar madatsar ruwa. Rabi'u Babale, wani magidanci da ruwa ya cinye unguwarsu ya ce sun shiga mawuyacin hali. Ya ce: "Haka muka kwana muka wuni ,ba mu samu  rintsawa ba, wadansu mun kasa cire su a cikin gidaje... Ruwan jiya na kaiwa wuya in kuma mutun na da tsawon yana kaiwa Kirji, amma yanzu Alhamdulillah yana kaiwa Kwankwaso..”  

Karin bayani:Rusau sakamakon ambaliya a Maiduguri

Ana fargabar cewar wasu fursunon sun tsere daga gidan gyaran hali na Maiduguri sanadiyyar ambaliyar ruwa, lamarin da ake ganin zai iya haifar da koma-baya ga zaman lafiya da aka samu. Haka kuma, mutane sun shiga damuwa saboda yadda namun daji da wasu dabbobi suka tsere daga gidan ajiye su, wanda ake ganin za su iya cutar da al'umma.

Gwamnati za ta taimaka wa wadanda ambaliya ta shafa

Kashim Shettima ya ce Maiduguri don jajanta wa wadanda ambaliya ta shafaHoto: Ken Ishii/REUTERS

Mataimakin shugaban Kasa Kashin Shetima ya ce gwamnati tarayya za ta hada kai da jihar Borno don taimaka wa wadanda matsalar ambaliya ruwa ta shafa. A lokacin da ya je duba wadanda  suke zaune a sansannin ‘yan gudun hijira bayan da ruwa ya ci gidajensu, Shetima ya ce: "Akwai hakkinku a kanmu, kuma hakkinku nan shi ne muga cewa mun tallafa muku. Duk abin da ya cancanta a yi za mu yi don mu share hawayenku. Muna muku godiya bisa ga halayen dattaku da kuka nuna, kun yi imanin cewa wannan masifa daga ubangiji ne kuma In Allah ya yarda zai share hawayenku....”

Damuwa a kan cututtukan da za su iya kunno kai

Kungiyar Grassroot Mobilizers for better Nigeria initiative na fadi tashin nemo taimakon al'umma da masu hannu da shuni inda suke dafa abinci domin raba wa al'umma da suka tagayyara. Aisha Abba Grema ta ce: "Gaskiya muna bukatar tallafi don mutane na cikin matukar 'yunwa. Mun fara karbar kayarn agaji daga Abuja na kayan sawa wato tufafi da kayan abinci.”

Karin bayani:Shekara guda bayan ambaliyar ruwa a Libiya

Babbar damuwa da ake nunawa ita ce ta barkewar cutuka saboda wannan ambaliyar ruwa, a dai ai lokacin gwamnatin jihar Borno ta sanar da rufe dukkanin makarantu har sai bayan makonnin biyu in lamarin ambaliyar ruwan ya yi sauki.