1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AIKIN GINA DANDALIN TUNAWA DA YAHUDAWAN DA `YAN NAZI SUKA KASHE A LOKACIN YAKIN DUNIYA NA BIYU.

YAHAYA AHMEDApril 13, 2004

A birnin Berlin, ana nan ana ci gaba da gina wani dandali, don tunawa da Yahudawan Turai da Hukumar Nazi ta halaka, a lokacin yakin duniya na 2. Za a dai kashe kimanin Euro miliyan 10 a kan aikin, wanda ake ta korafi a kansa a bainar jama’ar Jamus.

Berlin - Ma'aikata, a gun gina dandalin tunawa da Yahudawan da aka halaka a lokacin mulkin Nazi.
Berlin - Ma'aikata, a gun gina dandalin tunawa da Yahudawan da aka halaka a lokacin mulkin Nazi.Hoto: AP

A halin yanzu dai, tsakuwa ne ke zube a filin dandalin, inda kuma za a kakkafa wasu jigajigai na siminti masu tsayin mita 5. Wadannan jigajigan, su ne za su alamta dimbin yawan Yahudawan da Hukumar Nazi ta yi musu kisan kiyashi tsakanin 1939 zuwa 1945, wato lokacin da aka gwabza yakin duniya na biyu. Sai bayan an kakkafa duk jigajigan, wadanda yawansu ya kai dubu 2 da dari 7 ne, za a rufe duk filin dandalin da siminti, saboda jama’a maziyarta, su iya tafiya tsakanin wadannan dogayen sigogin. Wani Ba’Amirke, Peter Eisenman, ne ya tsara siffar dandalin. Game da yawan jigajigan da za a kakkafan kuwa, ya bayyana cewa, za su kasance ne a matse kusa da juna, don maziyartar da za su bi tsakaninsu su ji a jika, irin matsin da Yahudawan suka sami kansu a ciki, kafin a halaka su.

Gina dandalin kamar yadda aka siffanta shi dai, ba karamin aiki ba ne. Saboda wasu jigajigan a karkace suke. Amma haka Peter Eisenman, wanda ya tsara su, ke son su kasance. Frank Böhme, wani safiyo ne da ke kula da kakkafa jigajigan a dandalin. Ya auna duk fadin filin da na’urorinsa na safiyo. Daga bisani ne ya zayyana duk inda za a sa harsashin siminti, kafin a fara aikin kafa jigajigan. Girman dadndalin dai, gaba daya, idan an kammala aikin, zai kai filin wasan kwallon kafa guda biyu.

Ban da haka kuma, za a gina wasu zauruka a karkashin kasa, wato karkashin dandalin, inda a nan ne za a dinga bai wa maziyarta bayanai kan irin danyen aikin da `yan Nazi suka gudanar. A kan bangon daya daga cikin zaurukan ne, za a rubuta sunayen miliyoyin Yahudawan da aka halaka karkashin mulkin Nazin. Wannan kuma zai kasance wani gagarumin aiki ne da za a dade ana yinsa. An dai kiyasci cewa, idan maziyarci zai karanta duk sunayen daya bayan daya, to zai shafe tsawon shekaru 15 ba tare da ya motsa ba, kafin ya kammala.

Masu aikin gine-ginen dai na taka tsantsan wajen ganin cewa, komai ya ta fi daidai kamar yadda aka tsara. Klaus Merker, na daya daga cikin masu kula da sa harsashin jigajigan. Ya bayyana cewa:-

"Aikina dai shi ne na karshe kafin a kafa ko wane jijjige a kan harsashensa. Ya kamata in ga cewa kome ya kasance daidai kamar yadda aka auna. Wannan kuma aikin mutum daya ne. Gaba daya, zan kula ne da harsashin jigajigai dubu 2 da dari 7."

A karkashin harsashin, da jigajigan ne, zaurukan nunin za su kasance. Sabili da haka ne kuwa ake daukan duk matakan ganin cewa, nauyinsu ba zai sa su burma cikin zaurukan ba, bayan an kammala aikin. Akwai jijjige daya mai nauyin tan 15. Wannan shi ne ya fi sauran duk nauyi a dandalin. Ban da hakan, sai kuma an yi la’akari da nauyin siminti da karafun harsashin. Ga dai yadda wani ma’aikaci, Herr Bährmann, ya bayyana yadda suke tafiyad da wannan aikin:-

"A ko wace rana, muna zuba yawan siminti na kubik mita dubu da dari daya. A duk tsawon lokacin da muke zuba simintin kuwa, akwai wani can a karkashin kasa, wanda yake lura da ganin cewa, simintin ya zuba inda ake bukata, bai tsiyaye ya bi wani wuri daban ba."

A ran 8 ga watan Mayu na shekarar badi ne ake sa ran za a yi bikin bude dandalin. Wannan ranar dai, za ta zo daidai ne da cika shekaru 60 da kawo karshen yakin duniya na biyu. Saboda korafin da aka yi ta yi kan batun gina dandalin dai, sai da aka shafe shekaru goma ana ta muhawara, kafin Majalisar Dokokin Tarayya ta Bundestag, ta tsai da shawarar gina dandalin. A cikin watan Yunin shekarar 1999 ne, bayan wata muhawara mai tsananin da aka yi, magoya bayan ra’ayin gina dandalin, suka sami rinjayi a kuri’ar da aka ka da a Majalisar dokokin. Duk da hakan ma, sai a shekarar bara ne aka fara ayyukan ginin takamaimai.