Aikin Hajjin bana na gudana cikin nasara
October 9, 2013Maniyatan Aikin hajjin wannan shekarar ta 2013 daga sassa daban daban na duniya na kammala zamansu na ziyara a birnin Madina, inda suke daukar harama zuwa garin Makka don gudanar da Umrah da kuma Hajji nan da 'yan kwanaki masu zuwa.
Ana dai kyautata tsammanin maniyyata sama da miliyan biyu ne daga kassahen duniya za su gudanar da aiki Hajji na wannan shekara.
Duk da yake hukumomin kasar Saudiya sun rage yawan maniyyatan aikim Hajjin wannan shekara da kashi 20 a cikin 100, yanzu haka garin Madina sai tsiyayawa yake saboda ya zuwa yanzu kusan duk alhazzan duniya sun kammala ziyarce ziyarce a birnin Madina kuma sun isa birnin Makka ko kuma suna bisa hanya.
Na samu jin ta bakin wasu maniyyata daga Najeriya akan zamansu na Madina da kuma shirin da suke dashi na wucewa birnin makka
Su ma maniyyata mata ba a barsu a baya ba zuwa wajen Ibada, kuma sun bayyana gamsuwa da zamansu na garin Madina.
Riga kafin kamuwa da mura mai tsanani
Wani abu da hukumomin Saudiya suka karfafa wa maniyyata yin kaffa kaffa dashi kuwa shi ne akan bullar wata cutar mura mai tsanani da ke iya yaduwa ga alhazzai wanda ya zuwa yanzu shekara daya da bullowarta ta kama mutane fiye da 130 a cikin kasashen larabawa 8.
To ko wane tanadi ne hukumomin lafiya na Najeriya suka yi don kaucewa maniyyatansu kamuwa da irin wadannan cututtuka? Dakta Bello Abubakar wani likitan alhazzai ne a Najeriya, kuma ya ce sun dauki dukkan matakan da suka wajaba.
Su kuma jami'ai na hukumomin alhazzai na jihohi sun bayyana irin kokarin da suka yi na ganin an samu nasarar aikin wannnan shekerar.
Hukumomin Saudiya dai sun bayyana ranar Litinin mai zuwa 14 ga watan Oktoba ta kasance ranar Arafat wanda take ita ce kololuwar kammala aikin Hajji, bayan soma aikin Hajji a ranar 13 ga watannan, domin tashi zuwa gari Mina.
Mawallafi : Aminu Abdullahi Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh