1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bazata a tantance ministoci

Uwais Abubakar Idris/YBOctober 13, 2015

Majalisar dattawa ta fara aikin da karin mutane 16 da shugaban Najeriya ya mika.

Nigeria Bukola Saraki
Sanata Bukola Saraki shugaban majalisar dattawan NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Shugaban majalisar datawan Sanata Bukola Saraki ya fara ne dai da karanta jerin sunayen mutane 16 da shugaban Najeriya ya sake mika wa majalisar domin ta tantancesu da suka hadar da sunaye kamar haka: Khadija Bukar Abba Ibrahim da Birgediya Janar Mansir Dan Ali da kuma Zainaba Shasuna Ahmed daga jihar Kaduna, sai Aisha Bello da Pastor Usani Usani Ubani.

Daya bayan daya dai aka rinka kiran mutanen da aka tantance inda ‘yan majalisar suka rinka yi masu tambayoyi suna bada amsa.

Rotimi Amaechi tsohon gwamnan Rivers da shirin tantance shi ke daukar hankaliHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi

Ba kamar yadda aka zata ba aikin tantance mutane ya tafi cikin raha da annashuwa, abinda ma yafi daukan hankali shi ne yadda majalisar ta daga kafa ga sakataren jam'iyyar APC Alhaji Lai Muhammad wanda duk da cewa bai taba zama dan majalisa ba amma kuma suka amince da ya duka domin nuna girma, ya tafi ba tare da an yi masa tambayoyi ba.

Aikin tantance ministocin dai ya dauki hankalin al'ummar Najeriya sosai musamman yadda aka fuskanci korafe-korafe a wasu jihohi har ma da zanga-zanga.

Ginin majalisar dokoki a Abuja NajeriyaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Majalisar dai ta kwashe sao'i fiye da bakwai suna wannan aiki, inda ya zuwa yanzu suka tantance mutane 10 da suka hada da Cif Audu Ogbeh da Kayode Fayemi da Ogbunayya Onu da ma Janar Abdurrahman Dambazau. A ranar Laraba za'a ci gaba da wannan aiki.