1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin tawagar sa ido a Siriya ya kare

August 19, 2012

Rashin mutunta tsagaita wuta a Siriya ya tilastawa Majalissar Dinkin Duniya jinye tawagarta a kasar.

epa03224209 Moroccan Colonel Ahmed Himmiche (R) of the United Nations observers mission in Syria receives Babacar Gaye (L) military adviser to UN Secretary Ban Ki-moon, in Damascus, Syria, 18 May 2012. The chief of United Nations military observers in Syria Major General Robert Mood said on 18 May violence has increased this week in the country despite the increasing number of observers deployed to monitor the ceasefire. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
General Babacar Gaye shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya a SiriyaHoto: picture-alliance/dpa

Tawagar da Majalissar Dinkin Duniya ta aika domin sa ido ga rikicin Siriya, ta kawo karshen wa'adinta a Lahadi da misalin karfe 12 na dare. A watan Aprilun da ya shude ne a ka kafa wannan tawagar domin saka ido ga kiyaye tsagaita wutar da manzo na musamman Kofi Annan ya gindayawa bangarorin biyu da ke rikici a kasar. Shugaban tawagar Janar Babakar Gaye dan asalin kasar Senegal,ya bayana cewar tun a cikin watan yuni ne tawagar ta tabbatar da babu mai biyaya ga wannan mataki na tsagaita wuta a kasar ta Siriya inda ya zargi bangarorin biyu da kisan fararen fulla. To saidai kawo yanzu babu wani tabbacin ko Majalissar Dinkin Duniyar zata aikawa da wata tawagar sa ido a kasar.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Usman Shehu Usman