Aikin 'yan jarida na samu koma ba a Duniya
April 20, 2016Talla
Ƙungiyar ta RSF wacce ta bayyana rahotonta na shekara a yau ta ce dalilian koma bayan da aka samu,na da nasaba ne da gallazawa da 'yan jaridu ke fuskanta a duniya a cikin ƙasashe kamar su Turkiyya da Masar da Burundi da Libiya da Yemen da ma na Turai irisu Poland inda gwamnati ke yin katsa landan a cikin aikin 'yan jaridun
A karon Farko yankin Latine Amirka ya zo bayan Afirka a cikin Ƙasashe 180 saboda aikata kisa a kan 'yan jarida misali Banizuwela ta zo ta 139 yayin da Kwalambiya ta ke riƙe da matsayi 134.