1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An janye shari'ar Aminu

December 2, 2022

Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ta sanar da janye kara da kuma tuhumar da ta ke yiwa dalibin nan na jami'ar tarayyar da ke Dutse Aminu Mohammed.

Uwargidan shugaban kasan Najeriya, Aisha Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Akunleyan

Uwargidan shugaban dai ta sha suka daga bangaren kungiyoyin kare hakkin dan adama da ma sauran jama'a kan sanya wa da ta yi a kamo mata dalibin tare da lakadawa masa duka, saboda tuhumarsa da laifin bata mata suna a shafukan sada zumunta.

Yayin da yake gabatar hukuncin sakin Aminu, alkalin babban kotun Abuja Mai shari'a Yusuf Haliru, ya yi kira ga iyaye da su san ido wajen kula da harkokin 'ya'yansu don gudun aukuwar irin haka a nan  gaba.

An dai kame Aminu Muhammad ne a ranar 18 ga watan Nuwanban da ya gabata a jami'ar da yake a karatu, bayan da uwargidan shugaban kasar ta bayar da umurnin nemo mata shi sakamakon sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter makale da hotonta tare da cewa ta ci kudin Talakawa.