Aiwatar da musayar fursunonin Isra'ila da Falasɗinawa
October 18, 2011An fara musayar fursunoni da aka daɗe ana jira tsakanin Yahudawan Isra'ila da Falasɗinawa, inda a safiyar yau aka sa ɗaruruwan fursunonin Falasɗinu cikin bus waɗanda za a yi musayasarsu da sojan Isra'ila Glad Schalit. Hamas ta shirya gagarumin bikin tarban Falasɗinawa 477 da za a sako a yau ɗin. Bisa yarjejeniyar da aka cimma za a sako ƙarin falasɗinawa 550 bayan sojan na Isra'ila ya isa gida. Yarjejeniyar wanda ƙasashen Masar da Jamus suka jagoranci samar da ita, ita ce musayar fursunoni mafi girma da aka taɓa yi tsakanin ɓangarorin biyu. A halin da ake ciki masu shiga tsakani a tattaunawar Gabas ta Tsakiya na shirin ganawa da Isra'a da Falasɗinawa, domin duba yadda za a sake maido da tattaunawar ƙeƙe da ƙeƙe wanda ta ci tura kusan shekara guda. Masu shiga tsakani da suka haɗa da Tarayyar Turai da Rasha da Amirka za su gana da ɓangarorin biyu ne don jin bahasin ko wone ɓangare kafi a sake zama teburi guda.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal