1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shugaban kasa a Ajantina

Abdoulaye Mamane Amadou
October 28, 2019

A Ajantina dan takarar nan mai matsakaicin ra'ayin gaba-dai gaba-dai Alberto Fernandez ya lashe zaben shugabancin kasar tun a zagayen farko da sama da kaso 47.

Argentinien Christina Fernandez und Alberto Fernadez in Buenos Aires
Alberto Fernadez da mai dakinsa Christina Fernandez na murnar lashe zabeHoto: picture-alliance/AP Photo/D. Jayo

Fiye da kaso 80 cikin dari na kuri'un da aka rigaya akaa kidaya ya zuwa yanzu sun tabbatar da cewa Alberto Fernandez na kan gaba da sama da kaso 47, yayin da abokin hamayyarsa kuma shugaban kasar mai barin gado da tagomashinsa ya durkushe a shekarar bara bisa mummunan yanayi na karayar tattalin arziki, ya tashi da kaso 41.11 cikin dari.
 
Tuni dai Shugaba Mauricio Macri da ya sha kaye a zaben, ya taya abokin hamayyar tasa murna tare da bayyana cewar zai gudanar da adawarsa a cikin tsafta, inda ya gayyaci sabon zababben shugaban kaasar zuwa wani cin abincin rana a fadarsa ta shugaban kasa, gayyatar da tuni sabon shugaban ya amsa masa ita.

Sabon zababben shugaban kasar Alberto Fernandez ya ce babban abin da zai saka a gaba shi ne ganin ya kawo karshen halin taskun da 'yan kasar ta Ajantina suke fama da shi sakamakon tabarbarewar tattalin arziki.