1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ruwan sama ya haddasa barna a Kenya

Abdourahamane Hassane
March 9, 2026

Akalla mutane 45 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa bayan ruwan sama mai karfi a fadin Kenya.

Hoto: Felix Maringa/DW

'Yan sanda sun bayar da rahoton mutuwar akalla mutane 23 a babban birnin Nairobi kawai, yayin da kungiyoyin ceto ke ci gaba da fitar da gawawwaki da kuma taimaka wa mutanen da suka makale.Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya afkawa birnin Nairobi ya mayar da manyan hanyoyin birnin zuwa ambaliyar ruwa da ta mamaye dubban gidaje da kasuwanni.