An tsamo karin gawawwaki a hadarin alikofta a Legas
August 13, 2015Talla
Rahotanni daga Legas da ke kudu masu yammacin tarayyar Najeriya na cewa akalla mutane shida sun rasu a hadarin wani jirgin sama mai saukar ugulu a cikin teku a birnin na Legas. Tun a ranar Laraba an tsamo gawawwaki hudu sannan da safiyar wannan Alhamis an gano sauran guda biyu.
Jirgin na kamfanin Bristow na kasar Amirka ya taso ne daga wani wurin hakar mai amma ya yi hadari jim kadan kafin lokacin da ya kamata ya sauka.
Tuni dai mataimakiyar gwamnan jihar Legas, Idiat Oluranti Adebule ta je wurin da hadarin ya auku, sannan ta nuna cewa:
"Gwamnati na kula da lamari, tana jan ragamar al'amura za ta kuma rika ba da bayanai game da aikin ceto. Dukkan ma'aikatan ba da agajin gaggawa suna nan wurin suna kuma bakin kokarin shawo kan lamarin."