Akalla mutum 12 sun halaka a Peru
December 2, 2025
Akalla mutum 12 sun mutu a yayin da wasu 20 kuma sun jikkata a Peru bayan zaftarewar kasa ta nutsar da wasu jiragen ruwa biyu a kogin Ucayali, a yankin Amazon na kasar, ranar Litinin.
Hukumar lafiya a yankin ta ce har yanzu ana neman mutane biyu da suka bace, bayan faruwar lamarin da misalin ƙarfe 4:20 na safe a gogon yankin (0900 GMT) a tashar jiragen ruwa ta Iparia.
Mutum 18 sun mutu a hadarin mota a Peru
Jiragen ruwan biyu na kan hanyar zuwa wasu yankuna ne a bakin kogin da zaftarewar kasar ta auku ranar Litinin.
Tashar yada labarai ta gwamnati, mai suna Andina, ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sanda da sojojin ruwa sun tura jami’ai ta jiragen sama domin aikin ceto.
Zaben shugaban Peru zagaye na biyu
Hukumomi suka ce daga cikin fasinjojin jirgin akwai malaman makaranta da kuma likitoci wadanda suka rasa rayukansu.