1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Aki-Sawyerr ta lashe kyautar Gidauniyar Afirka ta Jamus

Usman Shehu Usman MAB
September 24, 2024

Mai rike da mukamin magajin garin Freetown Yvonne Aki-Sawyerr ta kasance “mai hangen nesa,” in ji Gidauniyar Afirka ta Jamus. A cikin shekaru shida, ta dora babban birnin Saliyo a kan turba mai dorewa.

Kyautar da Yvonne Aki-Sawyerr ta samu ta dace da aikinta a birnin Freetown na Saliyo
Kyautar da Yvonne Aki-Sawyerr ta samu ta dace da aikinta a birnin Freetown na SaliyoHoto: DW

Yvonne Aki-Sawyerr mace ce da ta taba aiki a duk bangarori. Magajiyar garin Freetown ta ciyar da birnin gaba a fannononi da yawa, lamarin da ya sa ta zama misali ga jagoranci. Babban misali shi ne yadda yanzu haka, babban birnin kasar Saliyo na Afirka ta Yamma ya samu cibiyar sarrafa ruwan sha bisa jagorancinta. An shigar da tankunan ajiyar ruwa 160 da tsarin tattara ruwan sama, baya ga aiwatar da tsauraran matakan kariya daga ambaliyar ruwa. Ana sarrafa shara da kuma bayan gida zuwa takin zamani da kuma makamashin gas da kuma gasa buluk na laka, kamar yadda Aki-Sawyerr ta bayyana. Wadanan matakan na taimakawa wajen kare dazuzzuka, saboda raguwar sare itatuwa don dafa abinci.

Aki-Sawyerr ta inganta rayuwa a Freetown

Batun samar da ruwan sha na birnin Freetown ma ya samu ci-gaba mai dorewa, inda wuraren tara ruwa suka kasance sanye da na'urori masu amfani da hasken rana , lamarin da ke bai wa al'ummomi da yawa damar samun ruwa mai tsafta a karon farko. A lokaci guda, wannan yana kara samar da 'yancin ga 'yan mata,  inda suke iya gudanar da kasuwanci ta kananan shaguna. Bugu da kari, barazanar da mata ke fuskanta na yade yayin diban ruwa ya ragu.

Karin bayani: Kyautar Nobel ga Abiy Ahmed

Yvonne Aki-Sawyerr na da kusance da jama'a a ko'ina ta samu kantaHoto: DW

Wannan abin ban sha'awar ne ya sa Yvonne Aki-Sawyerr ta cancanci lambar yabo daga Gidauniyar Afirka ta Jamus (DAS) ta 2024, a saboda jajircewarta na ci gaban birane da kuma shiga ana damawa da ita a al'amuran kula da birnin Frretown na Saliyo. Sannan ba ta saba wa alkawari, inda take bi mataki-mataki tana aiwatar da "hangenta na samar da jari mai dorewa cikin adalci". Gidauniyar mai zaman kanta ta gano cewa mai rike da mukamin magajin gari na da manufofi sosai fiye da yadda ofishinta ke bukata.

Ta zama abar koyi ga 'yan siyasa na Saliyo 

'Yar shekaru 56 a duniya, an haifi Yvonne Aki-Sawyerr a Saliyo kuma ta girma a kasar Ghana da Kanada. Bayan ta kammala karatunta, ta yi aiki a matsayin kwararriya a harkokin kudi da kuma mai duba kudi a birnin London na fiye da shekaru 25. Aikinta a ma'aikatar jama'a ta Saliyo ta fara ne da shigarta a lokacin barkewar cutar Ebola a 2014/2015. Amma a 2018, ta zama magajin garin Freetown, birni mai shekaru da yawa na yakin basasa. A watan Yuni 2023 ne aka tabbatar wa fitacciyar 'yar siyasar wa'adin mulki karo na biyu.

Ta samu nasarar aiwatar da manufofinta

Jami'an Gidauniyar Afirka ta Jamus sun yaba aiki dan Yvonne Aki-Sawyerr take yiHoto: DW

Aki-Sawyerr na samar da ayyukan yi da ba da damar saka hannun jari a fannonin yawon bude ido da sarrafa sharar gida da samar da ababen more rayuwa da tattalin arzikin marar gurbata mahalli, in ji Gidauniyar Afirka ta Jamus. Har ila yau, a fanni sufuri ma aana samar da ci-gaba da na'urorin zamani. Sannan mai rike da mukamin magajin garin ta ba da umarnin binciken yuwuwar samar wa birnin Freetown na kasar Saliyo  da motoci da ke amfani da wayar lantarki, wadanda ake amfani da su musamman a wurarin yawon shakatawa a kasashen da suka ci-gaba.

Bikin bayar da lambar yabo a ranar 16 ga Oktoba

Shugabar majalisar dokokin Tarayyar Jamus ta Bundestag Bärbel Bas ce za ta gabatar da lambar yabo ta Afirka ta 2024 ga 'yar kasar ta Saliyo a ranar 16 ga Oktoban 2024 a birnin Berlin. Aki-Sawyerr ta yi galaba a tsakanin gomman 'yan takara wadanda alkalai masu zaman kansu guda 20 suka hadu don tantancewa. Yvonne Aki-Sawyerr ta fadawa DW irin murnar da ta yi bayan da aka zabe ta, inda ta ce kyautar lambar yabon ba ta ita kadai ba ce, amma ta dukkan 'yan kasar Saliyo ne musamman ma daukacin abokanen aikinta.