1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan 'yan bindiga a Kudu maso gabashin Najeriya

Muhammad Bello MNA
November 30, 2022

Wasu 'yan bindiga a jihar Enugu da ke yankin Kudu maso gabashin Najeriya sun ayyana zaman gida na kwanaki 10 a wasu garuruwan al'ummomi da ke jihar.

Hoto: picture-alliance/dpa/G. Esiri

'Yan bindiga a yankin Kudu maso gabashin Najeriya, musamman na kungiyar rajin Biafra ta IPOB, su aka sani da kallafawa jama'ar yankin zaman gida na tilas a duk ranar Litinin da kuma ranar da duk jagoransu Nnamdi Kanu zai hallara a kotu.

Daga dukkan alamu 'yan bindigar dai sun kasa sun kuma tsare a yankin karamar hukumar Igbo-Eze ta Arewa da ke a jihar Enugu, sun umarci jama'ar da ke garuruwan Alor-Argu, Unadu, da Itchi da Ibagwa Aka, da Uhunowerri da dai sauransu da kada su kuskura su fita ko-ina kamar kullum, tare da cewar kowa ya zauna gida gami da cewar in kunne bai ji ba to jiki zai ji.

Karin bayani: Takkadama kan korar karar Kanu

Zaman gidan na kwanaki 10 da 'yan bindigar suka ayyana, sun ce dau wannan mataki ne, don yin zaman makoki na musamman ga 'yan kungiyar da dama da jami'an tsaro suka hallaka a yankin.

Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi

Tuni kuma 'yan bindigar suka fara kwace ababen hawa masu dauke da rajistar lambar Najeriya, sun umarci hukumomin makarantu da su cire tutocin Najeriya da kuma daina sa dukkanin wani kayan makaranta da ke dauke da kalolin fari da kore wato alamar Najeriya.

Wani dan asalin yankin na Kudu maso gabashin Najeriyar da ya nemi a boye sunansa, ya tabbatar da cewar kusan kullum sai 'yan bindigar sun dau rayukan jama'a a yankin.

Mata da dama da ke cikin garuruwan da 'yan bindigar da sau tari ake cewar ba a san su ba da kuma ma su lura da al'amura ke zargin 'yan kungiyar IPOB ne, yanzu sun zabi saka bakaken kaya, tare da gudanar da zanga-zangar bayyana halin rashin tsaro da suke ciki.

Aci Opaga, lauya ne a yankin ya yi magana kan halin da ake ciki.

"Matsalar ita ce, akwai karuwar tashe-tashen hankula nan da can a yankin a yanzu, kuma sai ka rasa wanda za ka zarga, kuma marasa da'a na amfani da damar takidin 'yan IPOB, suna aikata laifuka da dama. Gaskiya muna cikin matsala kwarai, kuma dole jama'a su bi umarnin tilasta zaman gida, don rayuwarsu ce gaba."

Ana danganta ayyukan 'yan bindigar da kungiyar IPOB ta Nnamdi KanuHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Da dama dai na tunanin ko me kungiyar hada kan kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo ke yi kan wannan garari na matasan yankin da ke karakaina dauke da manyan bindigogi suna halakawa tare da firgita jama'a? Chief Alex Chidozie Ogbonna, shi ne ke magana da yawun kungiyar.

"Yanayin akwai rikitarwa, tuni mu jama'ar yankin muka yi tir da batun umarnin zaman gida na rainakun Litinin tare da umartar jama'a da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum. Amma kuma 'yan bindiga na ci gaba da firgita mutane, kuma ba isassun jami'an tsaro da za su iya cimma su, ka ji inda matsalar take. Don haka jama'a dole ne su shiga fargaba, ba wai ta tilasta musu zaman gida ba, a'a sai dai fargabar rashin isassun jami'an tsaro da za su iya tunkarar 'yan bindigar."

Duk kokarin da wakilin DW a yankin ya yi na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Enugu musamman, wani Daniel Ndukwe, hakan ba ta samu ba.

An fi danganta 'yan bindigar yankin na Kudu maso gabashin na Najeriya da kungiyar rajin Biafra bangaren IPOB da Nnamdi Kanu da yanzu ke fuskantar shari'ar cin amanar kasa ke jagoran ta, da kuma kungiyar ESN da ke zaman wata rundunar tsaro ta sa kai. Sai kuma rundunar tsaron EBUBE AGU da gwamnonin yankin su biyar suka kafa tare da ba su makamai don aikin tsaro a fadin.